Bayan shan kaye hannun Atiku, Gwamnan PDP ya fara shirin kwace tikitin tazarce

Bayan shan kaye hannun Atiku, Gwamnan PDP ya fara shirin kwace tikitin tazarce

  • Bayan rashin nasara a zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, Gwamna Bala Muhammed na Bauchi ya fara shirin tazarce a kujerarsa
  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa dama can akwai 'Plan B' idan har gwamnan bai samu nasara ba a zaɓen fidda gwani ba
  • Sai dai shugaban jam'iyyar PDP reshen Bauchi ya musanta lamarin, ya ce kuskure aka samu sunan gwamnan ya fita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bauchi - Gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammed, wanda na ɗaya daga cikin yan takarar da suka sha ƙasa a zaɓen fid da gwanin PDP, ya koma yana son karɓan tikitin tazarce kan kujerar gwamna.

Wasu majiyoyi daga PDP da gwamnatin Bauchi sun tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa gwamna shi ne ɗan takarar PDP a jihar duk da bai shiga zaɓen fitar da ɗan takara ba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn

Tsohon Sakataren gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kassim, shi ne ya lashe tikitin takarar gwamna a zaben fidda gwanin da ya gabata na PDP.

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed.
Bayan shan kaye hannun Atiku, Gwamnan PDP ya fara shirin kwace tikitin tazarce Hoto: Senator Bala Abdulƙadir Muhammed/facebook
Asali: Facebook

Hassan Grema, wanda ya jagoranci gudanar da zaɓen, ya ayyana Kassim a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri'u 655 cikin 656 yayin da kuri'a ɗaya ta lalace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Hoto da sunan gwamna Bala Muhammed ya bayyana a jikin takardar sakamakon zaɓen wanda ya sa mutane cikin ruɗani.

Menene gaskiyar haka?

Yayin da yake martani ga tambayoyin yan jarida, shugaban PDP na Bauchi, Alhaji Hamza Koshe Akuyam, ya ce:

"A'ah ba gaskiya bane, Shi (Muhammed) bai sayi Fom ba, kuskuren fitarwa ne har sunansa ya bayyana a cikin takardar zaɓe."

Amma wata majiya ta ce akwai shirye-shiryen da aka yi na ba gwamna Muhammed damar tazarce idan ya sha kaye a zaɓen fidda gwani, kuma hakan ne ta faru.

Kara karanta wannan

Gwamnan Borno a 2023: Dan takarar PDP ya zargi Zulum da son kai, ya sha alwashin tsige sa daga mulki

Premium Times ta rahoto Majiyar ta ce:

"Ya jingina da abin da mutanen Bauchi suke so, ya nemi takarar shugaban ƙasa don amsa kiransu da sauran yan Najeriya. Yanzu ya koma hannun su, su yanke motsinsa na gaba."

Da aka faɗa masa tuni PDP ta kammala zaɓen fid da gwani na gwanoninta, majiyar ta ƙara da cewa, "Ba abin damuwa bane, duk abin da mutane ke so shi za'ai."

Haka zalika da aka tambayi majiyar ko gwamnan zai fafata a zaɓen 2023 domin neman tazarce kan kujerarsa, ya ce:

"Eh haka lamarin yake, kunsan cewa neman tikitin shugaban ƙasa wani karin kwarewa ne."

A wani labarin na daban kuma Bayan janye takara, Sanatan APC ya sauya sheka daga jam'iyyar zuwa PDP

Sanatan Kebbi ta tsakiya kuma tsohon ministan Abuja, Sanata Adamu Aleiru ya suaya sheka daga APC zuwa jam'iyyar PDP.

Da farko dai Sanatan ya tsame kansa daga zaɓen fitar da ɗan takarar Sanatan APC, inda ya zargi cewa an shirya magudi da damfara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mako ɗaya bayan Murabus, Ministan Buhari ya lashe tikitin gwamna a APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel