Ministan Buhari ya ba APC kyautar N20m duk da ya sha kasa a zaben Shugaban Jam’iyya

Ministan Buhari ya ba APC kyautar N20m duk da ya sha kasa a zaben Shugaban Jam’iyya

  • Sanata George Akume ya kai wa sabon shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ziyararsa ta farko
  • Ministan tarayyar ya bayyana cewa ya hakura da kudin da ya kashe wajen sayen fam din takara
  • George Akume ya na cikin wadanda suka janye takara a zaben APC na kasa bayan sun saye fam

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Benuwai, George Akume wanda ya yi takarar shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya hakura da kudin da ya kashe na sayen fam.

Jaridar Punch ta rahoto Sanata George Akume a lokacin da ya ziyarci babbar sakatariyar APC na kasa, ya na cewa ya ba jam’iyya kyautar N20m da ya biya.

Ministan harkokin na musamman ya kai wa sabon shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ziyara ta musamman a ofishinsa da ke birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Mahaifina Ya Min Gargaɗi Game Da Zuwa Ƙauyenmu, Ya Ce Mayu Za Su Cinye Ni, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa

Da yake amsa wata tambaya daga ‘yan jarida, Sanata Akume ya ce ya hakura da abin da ya kashe wajen sayen fam din shiga takara da na nuna sha’awar kujera.

Ba haka Buhari ya fada ba - Akume

Jaridar Daily Trust ta rahoto Ministan ya na cewa babu inda shugaban kasa ya bada umarnin a maidawa wadanda suka nemi takara kudin sayen fam dinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon gwamnan ya ce Mai girma Muhammadu Buhari ya kira su liyafa, inda ya yi kira ga duk mai neman matsayi ya hakura, a bar wa mutum daya kujerar.

'Yan Jam’iyyar APC
Taron zaben jam'iyyar APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

“Ba umarni aka bada ba, kun san shugaban kasa mutum ne da ya yadda da tsarin damukaradiyya. Na san wannan, zan iya tuna abin da ake yi a da.”
“Akwai bambanci na gaske tsakanin yadda shugaban kasa yake yin abubuwa, da kuma abin da mu ka gani tsakanin shekarar 1999 da 2007.” – George Akume.

Kara karanta wannan

Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m

Hadin-kai da zaben 2023

Babu abin da ya kawo batun kudi, Ministan tarayyar ya ce shi a karon kansa ya hakura da abin da ya biya, kuma ya na sa ran sauran ‘yan takara za su yafe.

An rahoto Akume yana mai cewa ya zama dole dukkaninsu su bada goyon baya domin ganin sababbin shugabannin jam’iyyar APC sun kai ga nasara.

A jawabin na sa, an ji George Akume yana cewa APC ta yi karfi a jihar Benuwai da za ta iya kifar da gwamnatin PDP a zaben da za a gudanar a shekarar 2023.

Jam’iyyar PDP ta samu miliyoyi

Kwanaki kun ji cewa daga lokacin da aka bude saida takara zuwa yanzu, magoya baya sun sayawa irinsu Atiku Abubakar, Bukola Saraki da wasunsu fam.

Kudin da jam’iyyar PDP ta ke samu daga saida fam din shiga takarar shugaban kasa ya na ta kara yawa. An samu kusan N280m a hannun 'yan takara bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel