Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m

Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m

  • Babban jigon APC na kasa, Sanata Bola Tinubu ya bayar da gudunmawar naira miliyan 50 ga wadanda harin jirgin kasa ya ritsa da su a Kaduna
  • Tinubu ya ce Najeriya na zubar jini, cewa ya zama dole a hada hannu don yakar ta’addanci a kasar
  • Dan siyasar ya ce abun takaici ne yadda azzaluman suka farmaki bayin Allah da basu ji ba basu gani ba

Kaduna - Jagoran jam’iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa, Bola Tinubu, ya koka kan yawan hare-haren ta’addanci da kasar ke fuskanta, inda ya ce Najeriya na zubar jini.

Tinubu wanda ya ziyarci jihar Kaduna domin yiwa gwamna Nasir El-Rufai jaje a ranar Talata, 5 ga watan Afrilu, ya ce akwai bukatar hada hannu domin yakar fashi da makamai da kuma ta’addanci.

Kara karanta wannan

Ramadan: Bola Tinubu ya yi kira na musamman ga al’ummar Musulmi a kan watan azumi

Ya yi Allah-wadai da harin da yan bindiga suka kai kan jirgin kasar Kaduna a makon da ya gabata, inda ya bayyana lamarin a matsayin abun kunya, Daily Trust ta rahoto.

Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m
Tinubu ya bayar da gudunmawar miliyan N50 ga wadanda harin jirgin kasa ya ritsa da su Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mai neman takarar shugabancin kasar a zaben 2023 ya kuma bayar da gudunmawar naira miliyan 50 ga waranda harin ya ritsa da su, rahoton Vanguard.

Tinubu ya ce:

“Muna fuskantar gagaruman matsaloli a yanzu haka kuma ya zama dole mu kara kaimi. Najeriya na zubar jinni a madadin kowa. Ya zama dole mu yaki ta’addanci da dukkan karfinmu da duk abun da muka mallaka. Ba abun kunya bane mutum ya kasance talaka, amma ba za a yarda da talauci a matsayin al'ada ba.
“Abun kunya ne mutum ya zamo mara hankali, mugu kuma azzalumi ko dan ta’adda mai saka tsoro a zukatan al’umma kuma hakan ba abun yarda bane. Na kawo ziyarar jaje ne jihar Kaduna domin yiwa Gwamna da mutanen Kaduna da na Najeriya baki daya jaje.

Kara karanta wannan

Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki

“Abun da ya faru da mutane a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin ya shafi dukkanmu. Ranar bakin ciki. Duk abun da ya faru da yan Najeriya ya faru da mu dukka. Na fahimci cewa har yanzu ba a ga wasu mutane ba. An farmaki bayin Allah, an kashe su, an jefa yan uwansu cikin halin kunci; abun takaici ne. Amma ya zama dole mu mika lamarin ga Allah.
“Malam El-Rufai, gwamnan, muna tafiya da kai a kowani bangare saboda kaine alamar da nuni ga hadin kai. Ba za mu manta da wannan ba cikin sauri. Alama ce ta hadin kan Najeriya. Batun hidima ne amma idan yan hana ruwa gudu na ganin za su iya haka yin wannan aiki da ci gaban jama’a, duk za mu ce a’a.”

Da yake martani, El-Rufai ya nuna godiya ga Tinubu kan soke bikin zagayowar ranar haihuwarsa karo na 70 domin karrama wadanda harin ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

A wani labarin, mun ji cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce kalubalen tsaro sun mamaye gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari fiye da zaton mai tunani.

The Punch ta ruwaito cewa, ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da aka tabbatar da mutuwar mutane a kalla mutum 7 tare da batan fasinjoji 21.

Obasanjo ya ce wannan mummunan al'amari ya nuna cewa ‘yan Najeriya ba su da tsaro a ko’ina – a cikin motoci, a jirgin kasa ko kuma a cikin jirgi. Ya ce kasar na cikin wani mawuyacin hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel