Tsohon Gwamnan PDP ya yi fatali da su Atiku da Saraki, zai marawa Wike baya a 2023

Tsohon Gwamnan PDP ya yi fatali da su Atiku da Saraki, zai marawa Wike baya a 2023

  • A zaben 2023 da ake shirin yi, Ayodele Peter Fayose ya na tare da Nyesom Wike a jam’iyyar PDP
  • Ayo Fayose ya bayyana cancantar gwamna Nyesom Wike da takara a lokacin da ya ziyarci Ribas
  • Tsohon gwamnan na Ekiti ya ce matsalar Wike daya ce, bai yi wa kalamansa wata kwaskwarima

Rivers - Ayodele Fayose wanda ya yi gwamna a jihar Ekiti a karkashin jam’iyyar PDP ya na goyon bayan takarar gwamna Nyesom Wike a zaben 2023.

Ayodele Fayose ya yabawa Nyesom Wike, ya ce mutum ne shi mai halin kwarai. Jaridar Premium Times ta fitar da wannan rahoton a ranar Larabar nan.

Tsohon gwamnan na Ekiti ya ce a matsayinsa na dattijo, ya san abin da ya kamata, don haka ya jinjinawa Wike a lokacin da ya ziyarce sa a Fatakwal.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Sanata Kwankwaso ya aikawa Jam’iyya takardar barin PDP, ya bayyana dalilansa

Rahoton ya ce Fayose ya yi wannan bayani a lokacin da wasu mutanen Wike su ka gabatar masa fam din shiga takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

Abin da ya sa Fayose ya bi Wike

A jawabinsa, Fayose ya fara bayani ne abin da ya zo a cikin littafin addinin kiristoci na Injila.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jagoran na jam’iyyar PDP mai hamayya ya bayyana cewa gwamna Wike bai da boye-boye wajen magana, amma ya ce hakan bai hana shi zama nagari ba.

Tsohon Gwamnan Ekiti
Nyesom Wike da Ayo Fayose Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Wannan mutumi mai ban tsoro, Wike yana da zuciya mai kyau. Matsalar shi dai kawai yadda abu yake, haka yake fadansa, babu kwaskwarima.”
“Amma ba a yi wa mutum hukunci da kalamanshi kurum, domin kuwa akwai mutane da-dama da suke shiru-shiru ne, amma asalinsu mugaye ne.”

- Ayo Fayose

Kara karanta wannan

Zan janye daga takarar shugaban ƙasa bisa sharaɗi ɗaya, Gwamnan dake mafarkin gaje Buhari a 2023

Zan maida maku kudin ku - Fayose

Jaridar ta rahoto Fayose yana mai cewa shi karon kansa ya na da sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa, amma ya so a ce shi ya sayawa Wike fam.

Haka zalika tsohon gwamnan ya ce zai maidawa wadanda suka sayawa gwamnan fam kudin da suka kashe, ya ce za su hadu a filin zaben tsaida ‘dan takara.

Za a iya ganin duk abin da ya faru a shafin Mai girma gwamnan na jihar Ribas na Facebook. A na sa bangaren, Wike ya ce babu wanda ya isa ya yi masa magudi.

Kwankwaso ya koma NNPP

A Afrilun 2021 wani rikicin cikin gida ya barke a kan kujerun shiyyoyi na jam’iyyar PDP. Ku na da labari cewa wannan rikici ya sa Rabiu Kwankwaso ya bar PDP.

Tsohon Gwamnan ya ce ya rungumi jam’iyyar NNPP ne bayan ya yi kusan shekara 1 ya na jiran a zauna da jagororin PDP na Najeriya, amma hakan bai yiwu ba.

Kara karanta wannan

Masu neman mulkin Najeriya a PDP sun karu, Gwamnan Ribas ya shirya gwabzawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel