Ainihin abin da ya sa Gwamnan Anambra ya nemi ya shilla Amurka a ranar da ya bar ofis

Ainihin abin da ya sa Gwamnan Anambra ya nemi ya shilla Amurka a ranar da ya bar ofis

  • Patrick Ikwueto ya yi karin haske a kan abin da ya sa Willie Obiano ya yi yunkurin barin Najeriya
  • Lauyan ya ce tsohon gwamnan yana sauri ya je Amurka ne domin yana bukatar ya ga likitansa
  • Ikwueto ya ce Obiano ya dade yana jinya a wani asibiti a garin Texas, ba wai tserewa ya yi niyya ba

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya bayyana abin da ya sa ya yi yunkurin ficewa daga Najeriya a ranar da ya mikawa magajinsa mulki.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto na musamman a ranar Lahadi, inda aka ji abin da ya jawo aka yi ram da tsohon gwamnan a filin jirgin sama na Legas.

Da yake magana ta bakin lauyansa, Patrick Ikwueto SAN, Willie Obiano ya bayyana cewa yana bukatar ya yi maza ya ga likita ne lokacin a asibitin Amurka.

A cewar Patrick Ikwueto, tsohon gwamnan ya shiga wani mummunan yanayi wanda ya bukaci ya samu ganin kwararren likitan mafitsara a birnin Texas.

Ikwueto SAN ya musanya zargin cewa ‘dan siyasar yana kokarin kauracewa binciken EFCC ne.

Ba guduwa zai yi ba - Lauya

“A kan wani dalili zai tsere yayin da iyalinsa suke nan? Gaskiyar maganar ita ce shi Obiano yana da larura ne da yake bukatar ya gana da likitansa.”

- Patrick Ikwueto

Gwamnan Anambra
Jirgin Air Peace a jihar Anambra Hoto: @flyairpeace
Asali: Twitter

Kamar yadda wani rahoto ya nuna Obiano zai hadu da likita ne a asibitin Spring Creek Urology Specialists LLC da ke Houston, birnin Texas, a kasar U.S.A.

Tun ba yau, Obiano ya na zuwa a duba shi a wannan babban asibitin a cewar lauyan na shi.

Ba yau Obiano ya saba zuwa asibiti ba

“Saboda yanayin ciwonsa, tun a Yunin 2021 yake ganin likita a asibitin kwararrrun. An yi da shi zai yi jinyar karshe na makonni takwas a Houston.”
“A Disamban 2021 ya je asibiti, sai aka sa rana cewa zai koma a watan Maris dinnan, jim kadan bayan ya mikawa Soludo mulki.” – Patrick Ikwueto.

Ikwueto bai iya bayyana cutar da ta ke damun ‘dan siyasar ba. Amma jaridar ta ce ana rade-radin Obiano ya kamu da cutar kansa ne tun a farkon shekarar bara.

Iyalan 'Yan siyasa masu takara

Ku na da masaniya cewa a lokacin da Willie Obiano yake kan karagar mulki ne ya tabbatar da cewa Ebelechukwu Obiano za ta nemi Sanatar Anambra ta Arewa.

Da alama cewa Mai dakin tsohon gwamna Obiano, Ebelechukwu Obiano za tayi takara ne a karkashin jam'iyya APGA mai mulkin Anambra a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel