Zafin addini: Yadda Osinbajo ke mu’amalantar Musulman kusa da shi - Ma’aikaciyar Aso Villa

Zafin addini: Yadda Osinbajo ke mu’amalantar Musulman kusa da shi - Ma’aikaciyar Aso Villa

  • An samu wata Hadimar Yemi Osinbajo ta yi magana a kan zargin da ake yi wa mataimakin shugaban kasar
  • Wasu na jifan Farfesa Yemi Osinbajo da tsananin kishin addinin kiristanci ganin shi babban Fasto ne a coci
  • Dr. Balkisu Saidu ta ce ba haka abin yake ba, Osinbajo ba mutum ba ne da yake Fifita kiristoci a kan Musulmai

Abuja - Ana ta surutai a ‘yan kwanakin nan, ana zargin Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da zafin kishin addininsa na kiristanci.

Wata wanda ta yi shekara da shekaru ta na aiki da Farfesa Yemi Osinbajo, Balkisu Saidu, ta fito ta kare mai gidanta, inda ta bayyana cewa sam ba haka yake ba.

Dr. Balkisu Saidu ta maidawa masu wannan babban zargi martani ne a wani gajeren rubutu da ta yi wanda ya shiga shafin Sanata Babafemi Ojudu a Facebook.

Kara karanta wannan

Ku dawo mana da silalla, majalisar wakilai ta bukaci bankin CBN

A cewar Saidu, saboda tsabar adalcin mataimakin shugaban kasar, ba a yin taro a ofishinsa a Aso Villa a duk lokacin da ya san musulmai su na zuwa yin sallah.

Kamar yadda ta bayyana a rubutunta domin yin raddi, hadimar ta ce Osinbajo yana ware kudi daga alihunsa duk watan azumi domin yi wa musulmai buda-baki.

Ina zumbula hijabi na - Balkisu Saidu

Farfesa Osinbajo bai jin wani abu saboda ya ga Balkisu Saidu sanye da zumbulelen hijabi, kamar yadda bai da matsala don an yi wata shiga ta dabam a ofishinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Osinbajo ya bar Aso Villa
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: newswirengr.com
Asali: UGC

Farfesa Osinbajo yana aiki da kowa

A wajen rabon mukamai kuwa, Dr. Balkisu Saidu ta ce Farfesa Osinbajo yana tabbatar da cewa an bi doka musamman dokar nan ta FCC ta kason mukaman kasa.

Wannan ya sa mataimakin shugaban Najeriya yake da mukarrabai da masu taya shi aiki daga kowane yanki na kasar nan, kuma masu daraja da su ka san aiki.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari da Gwamnoni suka karbo bashin Naira Tiriliyan 6.64tr a cikin shekara daya

A karshe ta bada shawarar a daina biyewa abin da ta kira karyar ‘yan siyasa da ‘yan kanzaginsu wajen yayata wadannan jita-jita domin gudun fushin Ubangiji.

Dr. Saidu ce babbar mai taimakawa Osinbajo wajen harkar shari’a da bincike da bin ka’ida.

Shin da gaske ne abin da ake fada?

Legit.ng Hausa ta tuntubi wanda ya taba aiki da Osinbajo, aka tabbatar mana da cewa shakka babu, ya zagaye kan shi da kiristoci musamman ‘ya 'yan cocinsa.

“Wannan gaskiya ne, kuma hakan zai iya yi masa illa wajen zaben shugaban kasa. Na san wasu sun fara sukarsa a kan wannan."
Amma kuma yana daukar wadanda ya san za su yi masa aiki ne da kyau. Mun san kafin ya samu mulki, iya Legas kurum ya sani.”
“Asali ba ‘dan siyasa ba ne mai jama’a a kowane lungu a kasar nan.” Inji tsohon hadiminsa.

Babu maganar 'Dan Arewa a 2023

Kungiyar Arewa Concerned Civil Society Organization of Nigeria ta ce za tayi kokari wajen ganin ta yaki ‘Yan Arewa a zabe mai zuwa saoda a ba 'Yan kudu dama.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun mamayi Jami'an gidan Yari, sun halaka fiye da ɗaya

Kakakin wannan tafiya, Abdulsalam Mohammed-Kazeem ya ce da so samu ne wanda zai zama magajin kujerar Muhammadu Buhari a 2023 ya zama Inyamuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel