Ku dawo mana da silalla, majalisar wakilai ta bukaci bankin CBN

Ku dawo mana da silalla, majalisar wakilai ta bukaci bankin CBN

  • Yan majalisa sun ce ya kamata a dawo amfani da silalla la'alla tattalin arzikin kasar nan ya farfado
  • Majalisar ta bayyana cewa kowace shekara ana karban kudin buga silallan amma ba'a ganinsu a gari
  • An umurci bankin CBN ta wajabtawa bankuna amfani da silalla daga yanzu

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ranar Talata ta bukaci babban bankin Najeriya CBN ya dawo da amfani da kudin sillala a Najeriya.

Wannan ya biyo shawaran kudirin da Hanarabul Muda Umar ya gabatar a zauren majalisa, rahoton Tribune.

Ya yi bayanin cewa a lokacin tsohon gwamnan CBN, Sanusi Lamido Sanusi, an dawo da silalla N2, N1 da kwabo 50.

Bankin CBN
Ku dawo mana da silalla, majalisar wakilai ta bukaci bankin CBN

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan rasa damar shiga gasar kofin duniya, Najeriya ta fatattaki kocin Super Eagles

Yace:

"Majalisa ta lura cewa duk da makudan kudin da aka badawa na buga silalla, ba'a ganinsu a cikin jama'a."
"Majalisar ta lura cewa harkokin yau da kullum na yan Najeriya sun shafu saboda rashin silalla da kananan kudade wanda hakan ke janyo hauhawar tattalin arziki."
"Majalisa ta yi imanin cewa idan aka zuba kananan kudade da silalla cikin kasuwa, hakan zai taimaka wajen magance hauhawa da farfado da tattalin arziki."

Saboda haka, majalisar ta bukaci babban bankin ya wajabta amfani da silalla matsayin kudi kuma a tabbatar bankuna na amfani da su.

Majalisar ta baiwa kwamitin harkokin bankin hakkin tabbatar da hakan ya faru.

Legit ta tuntubi masanin harkokin tattali arziki kuma ma'aikacin bankin UBA, Mr Yusuf AbdulLateef, inda ya tofa albarkacin bakinsa kan wannan lamari.

A cewarsa, bai ga ta yadda wannan kira da majalisa ke yi zai rage hauhawar tattalin arziki ba.

Yace:

"Ni banga ta yadda zai yi tasiri kan hauhawar tattalin arziki ba. Dawo da silalla ba zai kara darajar kudi ba. Idan ina sayar da haja ta a N5, ko N10, do ka kawo Kobo 10 ko Kobo 20 ba zai sa in rage farashin kaya na ba."

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

"Ni banga wata alaka dake tsakanin hauhawar tattalin arziki da silalla ba. Abubuwan da ke haddasa hauhawar tattalin arziki shine sakamakon cutar COVID, kasashe sun saki kudade cikin jama'a, inda mukayi kuskure shine bamu saki kudin ta hanyoyin da ya kamata ba. Kudin basu isa ga mutanen da ya kamata su inganta tattalin arzikin ba."
"A Najeriya an zuba kudi, amma babu tasirin kudin da zuba."

Usman Yahaya Zaria ya bayyana cewa shi a ra'ayinsa wannan tsari ne mai kyau kuma ya bada shawaran a daina amfani da manyan kudi irinsu N1000 da N500.

A cewarsa:

Gaskiya naji dadin wannan labarin saboda za'a samu saukin Satan kudi kasa afita dasu, sannan Ina bada shawara a daina amfani da 1000 da 500, a koma 200 100. 50 20 10 5.
Kawai in akayi amfani da wannan shawara ta. Za'asamu mafita tattalin arzikin kasa zai bunkasa

Dinbin mutane za su rasa aikin yi yayin da Naira ta kara durkushewa kasa a kasuwar canji

Kara karanta wannan

Hayaniya ga muhalli: Kasar Ruwanda ta haramtawa musulmai kiran sallah da amsa-kuwwa

Jaridar Punch a wani rahoto da ta fitar, ta bayyana cewa karyewar Naira zai iya yin sanadiyyar da mutane masu yawa za su rasa hanyar cin abincinsu.

Maganar da ake yi a ranar Larabar nan shi ne Dalar Amurka 1 ta kai N590 a wajen ‘yan canji.

Kungiyar Manufacturers Association of Nigeria ta masu kere-kere a kasar nan ta ce jama’a za su rasa aikinsu a bangaren kere-kere da sauran harkoki.

Rahoton ya ce an tashi aiki a ranar Talata, 22 ga watan Maris 2022 yayin da Dala ta kai N585. Dalar £1 ta na N785. Abin ya kara muni ne a makon nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel