Atiku da Danmarke Sun Kwashewa Tinubu da Kwankwaso Mabiya 13, 000 a Katsina

Atiku da Danmarke Sun Kwashewa Tinubu da Kwankwaso Mabiya 13, 000 a Katsina

  • Jam’iyyun APC da NNPP mai alamar kayan marmari sun rasa jagorori da magoya bayansu zuwa NNPP
  • ‘Yan siyasa kimanin 13000 ne suka bar jam’iyyun nan, sun bi jirgin Lado Danmarke/Atiku Abubakar
  • Sanata Lado Danmarke ya karbi sababbin shiga jam’iyyar PDP wadanda za suyi wa PDP aiki a 2023

Katsina - Jam’iyyar APC mai mulki tana cigaba da rasa dinbin mabiya a jihar Katsina, ‘yan kwanaki kadan bayan Mustapha Muhammad Inuwa ya bar ta.

Rahoton da muka samu daga gidan talabijin na AIT shi ne PDP mai hamayya ta karbi mutane kimanin 13, 000 da suka sauya-sheka a karamar hukumar Jibiya.

Sanata Yakubu Lado Danmarke mai yin takarar gwamna a jam’iyyar PDP ya jagoranci karbar wadannan ‘yan siyasa da suka baro jam’iyyun APC da NNPP.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda ‘Yan APC Suka Wanke Wajen Gangamin Taron PDP a Wata Jahar Arewa

Da yake jawabi, Yakubu Lado Danmarke ya shaidawa sababbin shiga PDP cewa za a kula da su kamar yadda ake ji da sauran wadanda suka dade a jam’iyyar.

‘Dan takaran watau Sanata Danmarke ya sha alwashin gyara kura-kuran da ya kira na gwamnatin APC na kawo yunwa, talauci, matsalar tsaro da rashin cigaba.

Dalilinmu na barin APC - Magoya baya

Jagororin tawagar Aminu Maye Jibiya da Sa’adu Maigishiri Kaita sun shaidawa Duniya cewa rashin adalcin da aka yi masu a APC ne ya sa suka sauya-sheka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Katsina
Gangamin siyasa a Katsina Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Wanda ya yi magana a madadin jama’an ya koka a kan yadda gwamnatin APC tayi sakaci har rashin tsaro ya yi kamari a yankin Jibiya da aka sani da kasuwanci.

This Day tace sauran kusoshin siyasar Jibiya da Kaita da suka shigo PDP sun hada da Aminu Lawal, Lawal Abba, Nura Damaga, Mansur Mani da Basiru Isyaku.

Kara karanta wannan

Na Kusa da Gwamnan Arewa, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

Masu sauya-shekar sun ce sun gamsu da manufofin PDP don haka suka yi watsi da APC. A wajen taron, ‘yan siyasan na Katsina sun kona dubunnan tsintsiyoyi.

'Furofaganda' ce - NNPP

Legit.ng Hausa ta tuntubi shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Katsina, Hon. Sani Liti wanda ya shaida mata cewa furofagandar ‘yan siyasa ce kurum ba komai ba.

NNPP ta reshen jihar Katsina tace har zuwa yanzu ba ta san wasu ‘ya ‘yansu da suka bi PDP ba.

Tinubu zai yaudari mutane

An samu rahoto Dele Momodu yana cewa daga zaben 1993 Asiwaju Bola Tinubu ya dauko manufofin da ya tallatawa ‘Yan Najeriya domin su zabe shi a 2023.

Ana zargin ‘dan takaran na jam'iyyar APC ya tattaro dabarar MKO Abiola ta Hope 93, ya wanke komai, sannan ya jibge a takardar manufofinsa mai shafi 80.

Asali: Legit.ng

Online view pixel