Kusoshin APC sun yi maza sun ziyarci Sanatan APC ganin PDP sun fara jawo shi kusa

Kusoshin APC sun yi maza sun ziyarci Sanatan APC ganin PDP sun fara jawo shi kusa

  • Asiwaju Bola Tinubu da wasu ‘yan siyasa APC sun yi zama da Sanata Muhammad Danjuma Goje
  • Abdullahi Ganduje da Kashim Shettima su na cikin wadanda suka ziyarci tsohon gwamnan a gida
  • Ana tunanin jiga-jigan na APC sun kai masa ziyara ne da nufin hana shi sauya-sheka zuwa PDP

Abuja - Ganin akwai yiwuwar tsohon gwamnan jihar Gombe, Muhammad Danjuma Goje ya koma PDP, wasu manyan APC sun kai masa ziyara har gida.

Tribune ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris 2022 cewa jagoran APC, Bola Tinubu ya jagoranci ‘yan APC zuwa gidan ‘dan siyasar a Abuja.

Wadanda suka yi wa tsohon gwamnan na Legas rakiya sun hada da Abdullahi Ganduje na jihar Kano da tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.

Sanata Kashim Shettima mai wakiltar mazabar jihar Borno ta tsakiya abokin aikin Sanata Muhammad Danjuma Goje ne a majalisar dattawa na kasa.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin gwamna ya fice daga APC, ya bi sahun Kwankwaso zuwa NNPP

Jaridar Leadership ta tabbatar da wannan labari, ta ce an yi zaman ne a gidan Goje da ke Asokoro.

Ziyarar 'Yan PDP

Ziyarar ta zo ne kwanaki biyu bayan tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo da wasu jagororin adawa sun gana da Sanata Goje a gidansa.

Kusoshin APC
Bola Ahmed Tinubu a gidan Sanata Danjuma Goje Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

Sauran wadanda suka yi wa babban ‘dan siyasar tayin ya koma PDP sun hada da Ayodele Fayose, Nyesom Wike, Philips Aduda da kuma Hon. Hon. Ali Isa JC.

Rikicin APC a Gombe

Rahotanni sun bayyana cewa ziyarar ba ta rasa alaka da rade-radin da ake yi na sauya-sheka. Goje yana da dinbin magoya-baya a jihar Gombe da ya yi mulki.

Tsohon Ministan harkokin wutan ya samu matsala a siyasar gida a dalilin rikicinsa da Gwamna Inuwa Yahaya tun bayan da ya karba a hannun Dankwambo.

Kara karanta wannan

Siyasar Kaduna: ‘Yan gaban-goshin gwamna El-Rufai da za su kawo wanda zai gaji mulki

Sabanin Danjuma Goje da Yahaya ya sa wasu magoya baya su na ajiye mukamansu a APC a Gombe.

A ranar Asabar da ta wuce aka yi wannan zama na tsawon lokaci a cikin dare. Har zuwa yanzu babu labarin abin da ‘yan siyasar suka tattauna a bayan labule.

PDP a 2023

Dazu aka ji cewa Bukola Saraki, Bala Mohammed da Aminu Tambuwal sun yi zama a kan yadda za ta fishe su a zaben shugaban kasa mai zuwa a shekarar 2023.

‘Yan takarar za su yi zama domin shawo kan Atiku Abubakar domin a fito da 'dan takara ta hanyar maslaha ganin kowanensu ya cancanci ya karbi mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel