Rikici gabanin taron gangamin APC: Kujerar shugabancin jam'iyya ta raba kan Sanatoci

Rikici gabanin taron gangamin APC: Kujerar shugabancin jam'iyya ta raba kan Sanatoci

  • Kawunan sanatocin APC ya rabu kan zabin wanda zai dare kujerar shugabancin jam'iyyar na kasa
  • Akwai manyan sanatoci uku da ke neman kujerar wadanda suka hada da Sanata Tanko Almakura, Sanata Sani Musa da Abdullahi Adamu
  • Sai dai hankula da dama ya fi karkata ga Sanata Adamu saboda ikirarin da ake yi na cewa shine zabin shugaban kasa Muhammadu Buhari

Abuja - Batun wanda zai zama shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ya raba kan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a majalisa.

Sanatoci uku, Tanko Al-Makura daga Nasarawa, Sani Musa daga Neja da Abdullahi Adamu daga Nasarawa ne suke takarar kujerar.

Za a gudanar da babban taron jam'iyyar a ranar 26 ga watan Maris a Abuja, inda za a zabi shugaban jam'iyyar da sauran mambobin kwamitin uwar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Bode George: Zan tattara na koma Ghana sannan na dunga kallo daga nesa idan Tinubu ya zama shugaban kasa

Babban taron APC: Zabin shugaban jam’iyyar na kasa ya raba kan sanatoci
Zabin wanda zai zama shugaban jam’iyyar na kasa ya raba kan sanatoci Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa wani bincike da ta yi ya nuna cewa wasu sanatoci na goyon bayan Abdullahi Adamu saboda ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na goyon bayansa.

An tattaro cewa da dama daga cikinsu sun nuna goyon bayansu ga Adamu saboda yardar cewa babu wanda zai iya taka rawa a duk wani hukunci da shugaban kasar zai so ya dauka gabannin zaben 2023.

Wasu manyan sanatocin APC sun halarci taron kaddamar da ofishin kamfen din Adamu a ranar Alhamis a Area 11, Garki, Abuja, inda suka yi magana na goyon bayan takararsa.

Sun ce yana da kwarewa don jagorantar jam'iyyar.

Sanatocin da suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, shugaban masu rinjaye a majalisar, Yahaya Abdullahi, Bulaliyar majalisa, Orji Uzor Kalu, Adamu Aleiro da Ali Ndume.

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Bulaliyar majalisar wakilai, Mohammed Monguno ma ya halarci taron.

Ndume ya fada ma manema labarai bayan taron cewa yana goyon bayan Adamu ne saboda shi ya fi dukkanin masu takarar kujerar kwarewa da karfin gwiwa.

Ndume ya ce:

"Ina goyon bayan Abdullahi Adamu saboda shi ya fi cancanta da karfin gwiwa a tsakanin sauran yan takara.
"Adamu mutum ne da kudi ba zai iya juya shi ba. Ba ya tsoron fadin koma menene don kare abun da ya yarda da shi."

Daily Trust ta kuma rahoto cewa wani sanata da ya yi magana cike da karfin gwiwa ya ce:

"Shirin shine daura Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam'iyyar sannan Farouk Aliyu, tsohon dan majalisar wakikai daga jihar Jigawa ya zama mataimakinsa.
" Suna aiki tare da wasu mutane a fadar shugaban kasa don tabbatar da Rotimi Amaechi ya zama dan takarar shugaban kasa na APC.
"A bayyane yake karara shirinsu ya saba muradin yawancin yan jam'iyyar wadanda suke ganin mutum da ke gwagwarmayar gashin kansa ne ya kamata ya zama dan takara.

Kara karanta wannan

Yayinda Buni ya koma mulkinsa na APC, INEC tace yanzu zata halarci taron NEC na APC

"Sun riga sun gana da shugaban kasa sannan sun yi ikirarin cewa shugaban kasar ya amince da shirinsu."

Ku samar da sashin harkokin siyasa don tallata yan uwanku Musulmai, Tinubu ga shugabannin Musulunci

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya bukaci majalisar koli ta shari’a ta kasa da ta kafa wani sashi na harkokin siyasa domin wayar da kan mabiya addinin game da samar da shugaban kasa Musulmi a zaben 2023.

Da yake magana a taron kafin Ramadan na kungiyar ta SCSN, wanda aka gudanar a Osogbo, babban birnin jihar Osun, Tinubu ya ce Musulmai ba za su yarda a barsu a baya ba wajen shiga harkokin siyasar kasar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Yayin da yake neman goyon bayan kungiyar don cimma kudirinsa na son zama shugaban kasa, Tinubu, wanda ya samu wakilcin Asiwaju Musulumi na jihohin Yarbawa, Edo da Delta, Cif Tunde Badmus ya jaddada bukatar ganin Musulmai sun shiga lamuran siyasar kasar kamar sauran kungiyoyi.

Kara karanta wannan

2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

Asali: Legit.ng

Online view pixel