A buge da giya tazo min: Dalilin da yasa na waskawa matar Gwamna Obiano mari, Matar Ojukwu

A buge da giya tazo min: Dalilin da yasa na waskawa matar Gwamna Obiano mari, Matar Ojukwu

  • Matar marigayi jagoran yakin Biyafara, Ojukwu, ta yi bayanin abinda ya faru tsakaninta da matar Obiano
  • Bianca tace matar Obiano ta yi tatil da giyar Whiskey yayinda ta fuskanceta lokacin bikin rantsarwar
  • "A lokacin na mike don kare kaina kuma na waska mata mari don ta daina taba ni" tace

Ambasada Bianca Ojukwu, matar marigayi Chukwuemeka Ojukwu ta bayyana abinda ya faru tsakaninta da matar tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano.

Yayinda bikin rantsar da sabon gwamnan jihar Anambra Ebelechukwu Obiano da Bianca sun baiwa hammata iska.

Matar Ojukwu
A buge da giya tazo min: Dalilin da yasa na waskawa matar Gwamna Obiano mari, Matar Ojukwu Hoto
Asali: Twitter

A jawabin da ta saki ranar Juma'a, ta bada labarin abinda ya faru.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC, Bawa, ya yi martani kan kamen tsohon gwamna, zargin cin zarafinsa a siyasance

Tace:

"Abin mamaki, ta durfafo ni. Na yi tunanin gaishe dani tazo yi. amma kawai sai ta fara zagi na tana daga murya, tana tsokanata tana tambayata me ya kawo ni."
"Amma na share ta. Sai ta fara daura hannu kan kafada ta tana daga murya. Sai nace ta daina taba ni amma taki dainawa, ta fara kokarin cire min dan kwali. Wannan rainin hankali ne ga babbar mace iri na a al'adar Igbo."
"A lokacin na mike don kare kaina kuma na waska mata mari don ta daina taba ni."
"Abinda ya bani mamaki shine a buge take da giya. Na yi mamakin jin warin giya bakinta. Ta yaya uwargidar gwamna zata shigo taron rantsarwa a buge misalin karfe 9 na safe."

A kama Bianca Da Matar Obiano, Shahararen Lauya Femi Falana Ya Bayyana Laifin Da Suka Aikata

Shahrarren Lauya Mr Femi Falana (SAN), ya yi kira ga yan sanda su kama matar tsohon gwamna, Willie Obiano, Ebelechukwu; da tsohuwar jakadar Najeriya a Spain, Bianca Ojukwu, matar tsohon shugaban Biafra, Chukwuemeka Ojukwu.

Kara karanta wannan

Budurwa ta yi watsi da saurayin da ya kashe N1m don tafiyarta UK, ya fada tashin hankali

Falana ya furta hakan ne cikin sanarwar da ya aike wa The Punch a ranar Juma'a yayin da ya ke martani kan fadar da matan biyu suka yi a wurin rantsar da gwamnan Anambra, Farfesa Charles Soludo, a ranar Alhamis.

Babban lauyan mai mukamin SAN ya ce idan da ba manyan mutane bane su biyun da yan sanda sun kama su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel