A kama Bianca Da Matar Obiano, Shahararen Lauya Femi Falana Ya Bayyana Laifin Da Suka Aikata

A kama Bianca Da Matar Obiano, Shahararen Lauya Femi Falana Ya Bayyana Laifin Da Suka Aikata

  • Fitaccen lauyan Najeriya mai kare hakkin bil adama, Femi Falana, SAN, ya bukaci yan sanda su kama Bianca Ojukwu da Ebelechukwu Obiano
  • Falana ya bayyana cewa fadan da suka yi a fili laifi ne a karkashin doka kuma akwai hukuncin da aka tanadar masa don haka a cafke su
  • Lauyan ya kara da cewa rashin kama su nan take da ba a yi ba ya nuna akwai dokoki biyu a Najeriya, wato na talakawa da masu hannu da shuni

Lauya mai kare hakkin bil adama, Mr Femi Falana (SAN), ya yi kira ga yan sanda su kama matar tsohon gwamna, Willie Obiano, Ebelechukwu; da tsohuwar jakadar Najeriya a Spain, Bianca Ojukwu, matar tsohon shugaban Biafra, Chukwuemeka Ojukwu.

Falana ya furta hakan ne cikin sanarwar da ya aike wa The Punch a ranar Juma'a yayin da ya ke martani kan fadar da matan biyu suka yi a wurin rantsar da gwamnan Anambra, Farfesa Charles Soludo, a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna Obinao garin tserewa Amurka

A kama Bianca Da Matar Obiano, Shahararen Lauya Femi Falana Ya Bayyana Laifin Da Suka Aikata
A kama Bianca Da Ebelechukwu, Shahararen Lauya Femi Falana Ya Bayyana Laifin Da Suka Aikata. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Bianca da Ojukwu sun aikata laifi, ya kamata a kama su a tuhume su, Femi Falana

Babban lauyan mai mukamin SAN ya ce idan da ba manyan mutane bane su biyun da yan sanda sun kama su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa:

"Babu shakka, Gwamna Soludo ya bada hakuri bisa abin kunyan da aka tilastawa baki gani. Amma wannan ba shine karshen abin ba tunda an aikata laifin fada a bainar jama'a.
"Laifin fada a fili ya faru idan mutum biyu ko fiye da haka suka yi fada a fili. Laifi ne da aka tanadar wa hukunci a karashin sashi na 83 na dokar masu laifi.
"Ganin yadda ba a kama su ba saboda manyan mutane ne ya tabbatar cewa akwai dokoki kala biyu a Najeriya, na masu kudi da talakawa. Idan da ma'aikata biyu ne suka yi fada a wurin taron da an kama su, an tsare su an tuhume su da laifin kawo cikas na rantsar da gwamnan."

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel