Mai Mala Buni ya sake karbe rikon APC bayan wasikar da Buhari ya aikowa Gwamnoni

Mai Mala Buni ya sake karbe rikon APC bayan wasikar da Buhari ya aikowa Gwamnoni

  • Gwamna Mai Mala Buni ya koma ofishinsa na Shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya na kasa
  • Mala Buni ya rusa kwamitocin da Abubakar Sani Bello ya nada, za ayi aiki da tsohon kwamitoci
  • Shugaban jam’iyyar ya rage adadin ‘yan kwamitin CECPC da suke cikin babban kwamitin shirya zabe

FCT, Abuja - Shugaban APC na rikon kwarya na kasa, Mai Mala Buni ya sake tabbatar da kan shi a matsayin wanda rikon jam’iyya mai mulki ke hannunsa.

Legit.ng ta fahimci cewa Gwamna Mai Mala Buni ya fara daukar wasu matakai da suka sha bam-bam da wanda Abubakar Sani Bello ya dauka a makon jiya.

Shugaban kwamitin rikon kwarya da shirya zabe na CECPC, Mala Buni ya yi watsi da kananun kwamitocin nan da Gwamna Abubakar Sani Bello ya nada.

Kara karanta wannan

Rikici APC: Gwamna ya yi amai ya lashe, ya ce har yanzun Buni ne shugaban APC ta kasa

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello shi ne ya rike shugabancin jam’iyya a lokacin da aka samu sabani, har ya fito da wasu kwamitocin 20 da za su yi zabe.

Wadannan kananun kwamitocin aka ba alhakin tsara yadda za a shirya zaben shugabanni jam’iyya. Za ayi zaben ne a karshen watan Maris dinnan.

An taba babban kwamiti

Bala Buni ya cire sauran ‘yan kwamitin CECPC daga cikin babban kwamitin gudanar da zaben shugabanni, ya bar daga shi sai John James Akpanudoedehe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai Mala a Landan
Mai Mala Buni, Adamu Adamu da Shugaban kasa Hoto: @BuniMedia
Asali: Twitter

Sanata John James Akpanudoedehe shi ne sakataren kwamitin rikon kwaryan na CECPC. Daga shi sai shugaban rikon kwarya ne a cikin wannan kwamitin.

Za ayi aiki da tsohon kwamiti

Kwamitocin da Bello ya kafa sun tashi aiki yanzu a jam’iyyar APC. Vanguard ta ce za a komawa kwamitin ainihi mai mutane 1200 da Buni ya nada tun kwanaki.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta yi amai ta lashe, tace har yanzu Gwamna Mala Buni ne shugabanta

Abin da hakan ke nufi shi ne Gwamna Babajide Sanwo Olu da aka cire daga kwamitin yada labarai zai sake dawowa kwamitin, zai bar kwamitin harkar kudi.

Yahaya Bello zai koma kan kujerarsa na shugaban kwamitin tsare-tsare. Gwamna Abdullahi Ganduje zai canji Nasir El-Rufai kamar yadda aka tsara da farko.

Haka zalika irinsu Femi Fani-Kayode da aka yi waje da su daga kwamitoci za su koma. Alhaji Lai Mohammed ya rasa matsayin shugaba a kwamitin yada labarai.

Daga 1200 zuwa 107, zuwa 1200

A baya kun ji cewa Abubakar Sani Bello ya rage yawan ‘ya kwamitin da za su shirya zaben APC na kasa, daga mutane fiye da 1, 000, 'yan kwamitin sun dawo 107.

Akwai masu ganin mutanen da Buni ya zaba su yi aikin, sun yi matukar yawa. A wannan sauyi da Sani Bello ya kawo, gwamnan jihar Jigawa ne zai shirya zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel