Kafin a je ko ina, sabon shugaban APC ya zaftare ‘yan kwamitin zabe, daga 1200 zuwa 107

Kafin a je ko ina, sabon shugaban APC ya zaftare ‘yan kwamitin zabe, daga 1200 zuwa 107

  • Gwamna Abubakar Sani Bello ya canza yadda aka tsara ‘yan kwamitin zaben shugabannin APC
  • Sabon shugaban riko na jam’iyyar ta APC ya rage yawan ‘ya ‘yan kwamitin zaben da za a shirya
  • Daga mutane fiye da 1, 000, wadanda aka bari a kwamitocin gudanar da zaben sun dawo kusan 100

FCT, Abuja - Rahoton da jaridar The Cable ta fitar a ranar Laraba ya nuna jam’iyyar APC mai mulki tayi gyara a kwamitin zaben shugabanninta na kasa.

An samu wannan sauyi ne bayan gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya karbi rikon jam’iyyar daga hannun gwamnan Yobe, Mai Mala Buni.

Mala Buni ya zuba mutane kusan 1200 a cikin ‘yan kananan kwamitocin da za su yi aikin zaben shugabanni na kasa da aka tsara za ayi a karsen Maris.

Kara karanta wannan

Kwadayin 2023, Jonathan, FFK da abubuwa 5 da suka jawowa Buni matsala a tafiyar APC

Sabon shugaban kwamitin rikon kwaryan na APC, Abubakar Sani Bello ya ce mutanen da Buni ya lafta sun yi yawa a wajen gudanar da zaben shugabanni.

Rahoton ya ce a halin yanzu an zabi mutane 107 ne kadai su yi wannan aikin. A haka ba a hada da wadanda suke cikin babban kwamitin gudanarwa ba.

Sabon shugaban APC
Kwamitin zaben shugabanni na APC Hoto: @GovNiger
Asali: Twitter

An hada Badaru Abubakar da aiki

A wannan sauyi da Sani Bello ya kawo a makon nan, Mai girma gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar aka zaba ya jagoranci aikin.

Da yake rantsar da ‘yan kwamitin na gwamna Badaru Abubakar, Abubakar Sani Bello ya ce APC ba za ta iya jibga mutane da yawa a kwamitin zaben na ta ba.

Amma duk da haka Bello ya ce akwai bukatar a tafi da kowa a cikin kananun kwamitocin. Bello ya ce ragin da aka yi bai nufin an raina wasu ‘yan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Rikicin gida: Gwamnoni 6 da suka shiga suka fita, har suka ga bayan Mai Mala Buni a APC

Rahoton 21stcenturychronicle ya ce canjin da sabon shugaban jam’iyyar na kasa ya kawo, ya na nufin an cire mutane 893 daga aikin shirya zaben da za ayi.

“Mun rage yawansu zuwa adadin da za su yi iya aiki, ba tare da raina kowa ba, kuma ina tunanin wannan ya fi dacewa da jam’iyyarmu." - Bello.

Za a ga kusan duka kananun kwamitocin su na dauke ne da mutane hudu. Bayan shugaba wanda ake zaban wani babba a gwamnati, sai sakatare da mutane biyu.

An yi waje da Buni

Kamar yadda ku ka samu labari a baya, yadda John Odigie Oyegun da Adams Oshiomhole su ka kare, haka Gwamna Mala Buni ya rasa shugabancin APC ba ta dadi ba

Bayan an fatattaki Mala Buni daga shugabancin APC, tuni dai har Abubakar Sani Bello ya fara canza wasu abubuwan da tsohon shugaban ya yi a lokacin da yake ofis.

Kara karanta wannan

Sabon shugaban APC ya dauki matakin farko na dunkule jam’iyya kafin Buni ya dawo

Asali: Legit.ng

Online view pixel