Rudanin APC: An ce sakataren riko na APC na kasa yayi murabus, amma ya musanta batun

Rudanin APC: An ce sakataren riko na APC na kasa yayi murabus, amma ya musanta batun

  • Yayin da inuwar jam'iyyar APC ke ci gaba da dumama, sakataren riko na jam'iyyar ya lallaba ya fice daga cikinta
  • Har yanzu dai ba a san dalilin ficewarsa ba, amma ana danganta matakin nasa da rikice-rikicen da jam'iyyar ke fuskanta
  • Idan baku manta ba, a jiya ne gwamnan jihar Neja ya dale kujerar gwamnan Yobe ta shugabancin jam'iyyar

Wuse, Abuja - Sakataren kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa, tuni Akpanudoedehe ya kwashe dukkan kayan sa daga sakateriyar jam’iyyar ta kasa da ke titin Blantyre, Wuse 2 a babban birnin tarayya Abuja.

Sakataren riko na APC ya yi murabasu
Rikicin jam'iyyar APC: Sakataren riko na APC na kasa yayi murabus | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Duk da cewa ba a san dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar ba nan take, amma an gano cewa matakin nasa bai rasa nasaba da yadda ake tafiyar da jam’iyyar ba, inda wasu gwamnonin suka yi yunkurin tsige shi.

Kara karanta wannan

Yanzu: Bayan Shan Matsin Lamba Daga Mata, Majalisa Ta Canja Ra'ayinta Kan Dokar Mata, Za Ta Sake Sabon Kuri'a

Duk da cewa jami’an jam’iyyar da dama sun tabbatar da cewa Akpanudoedehe ya kwashe kayayyakinsa daga ofishinsa, amma ba su iya tabbatar da ganin wasikar da ke nuna ficewarsa ba, inji rahoton Vanguard.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shi ma Sanata Akpanudoedehe bai amsa kiran da aka yi masa ba domin jin ta bakinsa game da batun na murabus dinsa.

Ban yi murabus ba

Sai dai, a wata hira da jaridar Daily Trust, ya ce shi sam bai yi murabus ba.

A cewarsa:

“Na karanta a kafafen sada zumunta cewa na yi murabus daga mukamin sakataren jam’iyyar APC. Ina so in bayyana cewa ba gaskiya ba ne; cewa ban yi murabus ba. Idan na yi murabus, da kun ga takardar murabus da na rubuta. Wani ba zai ce wani ya mutu ba sa’ad da yake raye.

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

“Ban fi jam’iyya girma ba, ko shugaban kasa wanda shi ne jagora a kasa ba. Ina jiran shugaban kasa ya dawo."

Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani kan tsige gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka daga PDP

A wani labarin, jam'iyyar APC reshen jihar Ebonyi ta yi watsi da hukuncin babbar kotun tarayya dake Abuja, wanda ya kwace kujerar gwamna Dave Umahi da mataimakinsa, Dakta Kelechi Igwe.

Mutanen biyu sun rasa kujerunsu ne biyo bayan sauya shekar da suka yi daga PDP zuwa jam'iyyar APC, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Shugaban APC a jihar Ebonyi, Chief Stanley Okoro-emegha, da yake martani ne, ya ce alkalin Kotun ya tafka kuskure a hukuncin da ya yanke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel