Da Dumi-Dumi: Kwamitin raba mukamai ya mika rahoto ga sabon shugaban APC na ƙasa

Da Dumi-Dumi: Kwamitin raba mukamai ya mika rahoto ga sabon shugaban APC na ƙasa

  • Gwamnan Jihar Kwara ya miƙa rahoton kwamitinsa na tsarin raba mukamai ga shugaban rikon kwarya na APC ta kasa
  • Rahoto ya nuna cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, shugaban kwamitin ne ya mika rahoton ga gwamna Bello
  • Wannan dai na zuwa ne biyo bayan sauyin shugabanci da aka samu a kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC

Abuja - Kwamitin tsarin karba-karba ya mika rahoton tsara jadawalin raba mukamai ga sabon shugaban rikon kwarya na APC, gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ranar Litinin a Abuja.

Sakataren watsa labarai na gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas, Gboyega Akosile, shi ne ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sada zumunta Twitter.

Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, shi ne ya mika rahoton ga kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

Kwamitin mulkin karba karba ya mika rahoto
Da Dumi-Dumi: Kwamitin raba mukamai ya mika rahoto ga sabon shugaban APC na ƙasa Hoto: @GboyegaAkosile
Asali: Twitter

Rahoto ya nuna cewa gwamnan Kwara ya miƙa rahoton kwamitin nasa ne yayin taron kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, wanda gwamna Abubakar Bello ya jagoranta a Sakatariya ta ƙasa dake Abuja.

Mista Akosi ya ce:

"Gwamnan kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya miƙa rahoton kwamitin tsarin karba-karba bisa wa'adin da jam'iyya ta baiwa kwamitin kafin babban taron ƙasa dake tafe."
"Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ne ya karbi rahoton a madadin jam'iyyar APC ta ƙasa."

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da, gwamnonin jihohin Legas, Ogun, Imo, Gombe, Kogi da kuma jihar Borno.

Wannan na zuwa ne bayan canza shugabanci a kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC ta ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa an canza gwamna Mala Buni na jihar Yobe, inda aka maye gurbinsa da gwamna Abubakar Bello na jihar Neja.

Kara karanta wannan

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

A wani labarin kuma Gwamna Obaseki ya yi magana kan shirinsa na sauya sheka zuwa APC, ya shawarci shugabannin PDP

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya musanta rahoton dake yawo cewa ya fara shirye-shiryen komawa tsohuwar jam'iyyarsa APC nan gaba kaɗan.

Gwamnan ya ce bai taba tunanin ficewa daga PDP ba domin a cewarsa jam'iyyar ce ta lashe zaɓen jihar da ya gabata, kuma tana kan turban lashe kowane zaɓe a Edo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel