Gwamnan Bayelsa ya yabi Buhari, ya ce Shugaban kasa ya ba ‘Yan Najeriya ‘kyauta’

Gwamnan Bayelsa ya yabi Buhari, ya ce Shugaban kasa ya ba ‘Yan Najeriya ‘kyauta’

  • Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya ji dadin rattaba hannu a kan kudirin gyara dokar zaben kasa
  • Sanata Douye Diri ya yabawa Buhari, ya ce Shugaban kasa yana kaunar damukaradiyya ya daure
  • Diri ya yi kira ga duk kwamishinoni da hadimansa da suke harin 2023 su sauka daga mukamansu

Bayelsa - Mai girma gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya yabi shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin amincewa da kudirin gyaran zabe ya zama doka.

Jiya jaridar This Day ta rahoto Sanata Douye Diri yana cewa sa hannu da shugaban kasar ya yi a kan wannan kudiri ya nuna yana son damukaradiyya ta daure.

Gwamnan ya jinjinawa Muhammadu Buhari a wajen taron majalisar zartarwa na jihar Bayelsa da aka yi na wannan mako a gidan gwamnati da ke garin Yenagoa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Dan takarar shugaban kasa ya je neman shawari wurin Sheikh Gumi

A cewar Douye Diri, an zo karshen lokacin satar akwatin zabe, bangar siyasa da kawo hargitsi. Diri ya ce sabuwar dokar za ta zamanantar da yadda ake shirya zabe.

Jawabin Gwamna a taron SEC

“Ina so in yi amfani da zaman majalisar zartarwa na yau domin in yaba da kokarin Mai girma shugaban kasa, na sa kudirin zabe ya zama doka.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wannan ya kasance yana ci mana tuwo a kwarya a siyasarmu. Ta hanyar zabe na ake samun jagoranci na gari da kuma shugabanni na kwarai.”
Gwamnan Bayelsa
Shugaban kasa tare da Gwamna Douye Diri Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

“Shugaban kasa ya nuna yana son damukaradiyya ta dore a Najeriya da ya sa hannu a kudirin.” - Douye Diri

An yi wa 'Yan Najeriya kyauta

Rahoton ya ce Sanata Diri ya yabi shugaban kasar a madadin daukacin mutanen jihar Bayelsa, ya ce jama’a sun yaba da wannan aiki da kamar kyauta ne ga ‘yan kasar.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

“Idan a shekaru takwas da (Buhari) ya yi akwai kyautar da ya ba ‘Yan Najeriya, ita ce wannan.” - Douye Diri

Masu takara su yi murabus

Gwamna Diri ya yi kira ga ‘yan siyasan da ke neman kujerun gwamnati su guji tada hayaniya, ya kuma bukaci masu harin mukamai da su rubuta takardar murabus.

A karkashin sabuwar dokar zaben da aka sa wa hannu, dole ne duk wanda yake shirin yin takara ya sauka daga kujerarsa akalla watanni shida kafin a shirya zabe.

Rochas zai gaji Buhari?

A 'yan kwanakin nan aka ji Rochas Okorocha yana cewa idan ya zama Shugaban kasa za a ga canji, ya ce jama'a sun yi imani da shi saboda zai kawo hadin-kai

Sanata Okorocha ya ce zai sadaukar da rayuwarsa domin ya tabbatar kowa ya yi karatu kamar ‘dansa, kuma matasa za su samu abin yi muddin ya shiga Aso Rock.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Yadda Gwamnatin Jonathan ta so bankara doka domin hana Buhari mulki

Asali: Legit.ng

Online view pixel