Tsohon shugaban majalisa ya takalo fada da maganar tsige mataimakin Gwamnan Zamfara

Tsohon shugaban majalisa ya takalo fada da maganar tsige mataimakin Gwamnan Zamfara

  • Wani Sanatan Zamfara ya ja-kunnen Bukola Saraki, ya ce ya daina tsomo masu baki a harkar siyasa
  • Sanata Hassan Lawal Dan’iya ya fitar da wani jawabi na musamman, yana yi wa Saraki kashedi
  • ‘Dan Majalisar ya kare Bello Matawalle, ya ce sam ba a saba doka wajen tunbuke Mahadi Gusau ba

Zamfara – Punch ta rahoto Sanatan Zamfara ta yamma a majalisar dattawa, Hassan Lawal Dan’iya ya bukaci Bukola Saraki ya rabu da siyasar Zamfara.

Sanata Hassan Lawal Dan’iya ya fadawa tsohon shugaban majalisar dattawa ya guji jefa kansa a abin da ya shafi Zamfara tun da shi ba ‘dan jihar su ba ne.

Hassan Lawal Dan’iya ya fitar da jawabi na musamman, yana mai jan-kunnen Saraki musamman a kan abin da ya shafi tsige mataimakin gwamnan Zamfara.

Kara karanta wannan

Muhammad Hassan Nasiha: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

Sanatan ya ce sauke Mahdi Ali Gusau ya biyo bayan samun shi da cin amanar ofishin da yake kai.

“Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya fita harkar siyasar Zamfara, musamman a kan kalamansa a kan tsige mataimakin gwamna.”

Zamfara daban da Kwara

“Saraki wanda ya jahilci abubuwan da yake faruwa a jihar Zamfara ya san cewa Zamfara ba Kwara ba ce, saboda haka ya daina shigo mana cikin harka.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon shugaban majalisa
Abubakar Bukola Saraki Hoto: guardian.ng
Asali: UGC
“Yana yada karya ga ‘Yan Najeriya, yana cewa ba a bi doka wajen tunbuke mataimakin gwamna ba.”
“A matsayinsa na tsohon ‘dan majalisa da aka fi tunawa da rusa daular shekara da shekaru da Saraki ya kafa musamman a jihar Kwara da Najeriya, ya kamata ya yi bayanin dokar da aka saba a wajen tsige (mataimakin gwamnan jihar Zamfara.”

Daily Post ta rahoto Sanatan ya na kalubalantar tsohon gwamnan na jihar Kwara, ya ce ya fadi yadda majalisar dokoki ta saba doka wajen sauke Mahadi Gusau.

Kara karanta wannan

Zamfara: Sabon mataimakin gwamna Matawalle ya yi murabus daga kujerar Sanata

Sauya-shekar Matawalle

A cewar Dan Iya, jam’iyyar PDP ba ta ji dadin sauya-shekar gwamna Bello Matawalle zuwa APC, ya ce hakan ya jawo aka kai shi kara, kotu ta ba APC gaskiya.

‘Dan majalisar ya kare sauya-shekar Matawalle, ya ce don zabin kansa ya yi hakan, kuma Gwamnan bai taba tursasawa mataimakinsa ya bar PDP ba.

Shawarar Gwamna Tambuwal

Kwanaki kun ji cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya nuna cewa akwai abubuwan da jam’iyyar PDP ta ke bukatar yi kafin ta ci zabe.

Rt. Hon. Aminu Tambuwal ya yi wannan bayani ne bayan sakamakon zabukan da aka gudanar a Abuja, Imo, Ondo, Filato da kuma sauran jihohi kwana nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel