Buhari ya ki karbar shawarar Gwamnoni kan canza ‘dan takara a zaben shugabannin APC

Buhari ya ki karbar shawarar Gwamnoni kan canza ‘dan takara a zaben shugabannin APC

  • Wasu daga cikin gwamnonin APC sun nemi shugaban kasa ya sake tunani a kan Abdullahi Adamu
  • Muhammadu Buhari yana goyon bayan Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon shugaban APC
  • Da gwamnonin jihohi su ka kai wa shugaban kasar wannan batu a jiya, bai nuna amincewarsa ba

Abuja - Yunkurin wasu gwamnonin jam’iyyar APC na ganin Muhammadu Buhari ya canza shawara a game da Abdullahi Adamu a zaben APC ya ci tura.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu da wasu gwamnoni sun yi zama da shugaban kasa kafin ya tafi Kenya.

Wadannan gwamnoni na APC sun kawowa Muhammadu Buhari shawarar watsi da Sanata Abdullahi Adamu a matsayin ‘dan takarar shugaban APC na kasa.

Amma hakar gwamnonin ba ta cin ma ruwa ba, domin Mai girma Muhammadu Buhari ya nuna cewa yana nan kan bakarsa yayin da ake jiran ranar yin zabe.

Kara karanta wannan

Ranar babban taron APC na kasa na nan daram, Gwamnonin APC sun magantu

Buhari ya kafe

Wani rahoto da aka samu a This Day, ya nuna shugaban Najeriyar ya nuna yana goyon bayan Sanatan na Nasarawa ya zama shugaban APC ta hanyar maslaha.

Mai girma Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari da gwamnonin APC a Aso Villa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Gwamnoni 11 daga cikin 22 da jam’iyyar APC ta ke da su, sun nemi Muhammadu Buhari ya sake nazari a kan goyon bayan tsohon gwamnan na jihar Nasarawa.

Rahoton ya ce gwamnonin sun yi kokarin ganin an ba sauran ‘yan takara dama su shiga zaben shugabannin na kasa, amma Buhari bai karbi shawarar ta su ba.

Gwamnonin da suka je Aso Villa

Gwamnonin da aka yi wannan zama da su sun hada da: Kayode Fayemi (Ekiti), Aminu Masari (Katsina), Nasir El-Rufai (Kaduna), da Abubakar Badaru (Jigawa).

Yahaya Bello (Kogi), Hope Uzodinma (Imo), Gboyega Oyetola (Osun), Dapo Abiodun (Ogun), Sani Bello (Neja), da Umar Ganduje (Kano) sun halarci taron jiyan.

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

Jaridar ta ce mataimakin gwamnan Anambra, Nkem Okeke ya na cikin wadanda aka yi zaman da su.

Zabin Abdullahi Adamu

A makon da ya gabata ne aka ji shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince tsohon gwamna, Abdullahi Adamu ya karbi rikon jam’iyyar APC na kasa.

Mai girma Muhammadu Buhari ya nuna yana tare da Sanata Adamu duk da cewa sai daga baya ya shiga takarar. Sai dai Sanatan zai iya fuskantar wasu kalubale.

Asali: Legit.ng

Online view pixel