Magana ta kare: Buhari ya tsaida wanda yake so ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar APC

Magana ta kare: Buhari ya tsaida wanda yake so ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar APC

  • Ana shirin yin taro domin ayi zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa nan da kusan wata daya
  • Rahotanni sun ce Muhammadu Buhari ya zabi ‘dan takarar da yake so ya zama shugaban jam’iyya
  • Alamu su na nuna jagorancin APC zai koma hannun Sanatan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu

Rahoton da muka samu ya bayyana cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince tsohon gwamna, Abdullahi Adamu ya karbi rikon jam’iyya.

Wata majiya mai karfi har daga fadar wasu gwamnoni ta shaidawa Daily Trust cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya nuna yana tare da Sanata Adamu.

Shugaban kasar ya nuna inda ya karkata ne a wajen taron da ya yi da gwamnonin APC a Aso Villa.

Amma babu mamaki Abdullahi Adamu ya fuskanci adawa daga wasu masu neman wannan kujera da ake ta hange tun bayan sauke Adams Oshiomhole.

Sai a makon da ya gabata ne Adamu ya bayyana sha’awarsa na shiga zaben shugaban jam’iyya na kasa. Kafin nan ya rike shugaban kwamitin sulhunta na kasa.

Wani gwamna ya ce shugaban kasa ya ce shugaban jam’iyya zai fito ne daga Arewa ta tsakiya, kuma Adamu ya cancanta, kuma babu wanda ya yi masa gardama.

Shugabannin Jam’iyyar APC
Shugaba Buhari tare da su Abdullahi Adamu a Daura Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

An bar wasu su na kuka

Kafin Buhari ya sa baki, wasu daga cikin gwamnonin su na goyon bayan irinsu Tanko Al-Makura, Abubakar Bwari, wasu na tare da Sani Musa da George Akume.

Ministan ayyukan musamman, George Akume wanda yake harin wannan kujera, ya ce idan har za a fitar da ‘dan takara ta hanyar mubaya’a, shi ya kamata a tsaida.

Shi kuma Saliu Mustapha ya ce babu wanda aka tsaida a cikin ‘yan takarar. Sunny Sylvester Moniedafe ya ce idan har an zabi wani, ya kamata ne a zauna da su.

Ana kuma rade-radin cewa Ken Nnamani da Faruk Adamu Aliyu ne ake so a matsayin mataimakin shugaban APC na yankin Kudu da Arewacin Najeriya.

Leadership ta ce abun mamaki Sanata Abdullahi Adamu ne zai karbi ragamar jam’iyyar APC mai mulki daga hannun shugaban rikon kwarya, Gwamna Mai Mala Buni.

Kwankwaso sun raba kafa

A makon nan ne aka ji labari cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi karin-haske a kan kafa tafiyar TNM da zargin cewa ya fice daga PDP.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce har zuwa yanzu shi cikakken ‘dan jam’iyyar adawa ya PDP ne, ya ce a tafiyar The National Movement babu 'dan jam'iyyar da babu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel