Sarakuna 2 da ake ji da su, sun tsoma baki a cikin rigimar Bola Tinubu da Ministan Buhari

Sarakuna 2 da ake ji da su, sun tsoma baki a cikin rigimar Bola Tinubu da Ministan Buhari

  • Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III da Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi sun zauna da Rauf Aregbesola
  • Sarakunan na Oyo da Ife su na kokarin dinke barakar da ke tsakanin kusoshin APC a yankinsu
  • Ana sa ran kwanan nan a ga karshen rigimar Rauf Aregbesola da tsohon uban gidansa, Bola Tinubu

Oyo - Mai martaba Alaafin na kasar Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III da takwaransa na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi sun yi zama da Rauf Aregbesola.

Jaridar Leadership ta ce makasudin haduwar Sarakunan da Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne dinke barakar da ta ke cikin jam’iyyar APC.

An dade ba a ga maciji tsakanin Ogbeni Rauf Aregbesola da tsohon mai gidansa, kuma jagora a tafiyar APC a kudu maso yammacin kasar nan, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

Rahotanni sun bayyana cewa an soma wannan zama ne a gidan Mai martaba Sarkin Ibadan na Jericho da kusan karfe 10:00 na safiyar Talata domin a samu mafita.

Hadimin Ministan, Sola Fasure ya shaidawa Daily Trust cewa babu shakka Mai gidan na sa ya sa labule da suOba Lamidi Adeyemi da kuma Oba Adeyeye Ogunwusi.

Bola Tinubu da Ministan Buhari
Bola Tinubu da Ogbeni Aregbesola Hoto: an24.net
Asali: UGC

Me ake tattauna a kai?

Shi karon kansa mai ba Ministan shawara ya ce bai san abin da aka tattauna a wannan zaman ba.

A wani rahoto da ya fito daga The Cable, an ji cewa abokan siyasar Bola Tinubu da Rauf Aregbesola su na kokarin sasanta jiga-jigan na APC kafin 2023.

Abokan tafiyarsu su na ganin ya kamata a ajiye sabanin da aka samu a zaben Osun, a tunkari zaben shugaban kasa. Tinubu yana neman tikitin jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Sarakuna 2 sun karfafawa takarar Bola Tinubu, sun bayyana inda ya yi fice a siyasa

Ana ta kokarin ayi sulhu

Tun kafin jiyan, an ji kishin-kishin cewa manyan kasar Kudu (daga ciki har da Sarakuna da jagororin musulunci) za su baki domin ayi wa ‘yan siyasar sulhu.

Majalisar koli na shari’a watau NSCIA ta sa baki a rikicin Tinubu da Aregbesola. Tsohon gwamnan na Osun ya na rigima da Tinubu ne a kan zaben jiharsa.

Sai dai Tinubu bai samu halartar wannan zama da aka yi ba, amma a karshen taron an fara kai ga samun maslaha. An sa ranar da za a sake yin irin wannan zaman.

Yunkurin Act Now

Ana da labari cewa wasu magoya bayan Yemi Osinbajo na kungiyar ‘Act Now’ sun ziyarci Sarkin Sagamu, Tunde Ajayi domin mataimakin shugaban kasar ya yi takara.

Mai martaba Babatunde Ajayi ya shaida masu cewa babu dalilin a hurowa Farfesa wuta a kan neman mulki, inda ya ce Osinbajo ya san abin da ya fi dacewa a 2023.

Kara karanta wannan

Alkali ya bada umarni hukumar EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamnan APC a Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel