2023: Sarkin Yarbawa ya yi magana a kan Osinbajo, ya ce masoya su daina matsa masa

2023: Sarkin Yarbawa ya yi magana a kan Osinbajo, ya ce masoya su daina matsa masa

  • Wasu magoya bayan Yemi Osinbajo na kungiyar ‘Act Now’ sun ziyarci Sarkin Sagamu, Tunde Ajayi
  • Wadannan matasa su na so mataimakin shugaban kasar ya yi takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa
  • Mai martaba Babatunde Ajayi ya shaida masu cewa babu dalilin a hurowa Farfesa wuta a kan takara

Ogun - A ranar Litinin, 28 ga watan Fubrairu 2022, shugaban sarakunan jihar Ogun, Babatunde Ajayi ya yi magana game da Yemi Osinbajo da shirin 2023.

Mai martaba Akarigbo na kasar Remoland, watau Babatunde Ajayi ya bayyana cewa mutane su daina matsawa Farfesa Yemi Osinbajo kan sai ya yi takara.

Jaridar Daily Trust ra rahoto Oba Babatunde Ajayi yana cewa a kyale mataimakin shugaban kasar ya yi wa kansa zabi game da neman kujerar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Atiku Ya Kai Wa Obasanjo Ziyara a Gida, Sun Keɓe Suna Ganawar Sirri

Oba Ayaji wanda yake rike da mulkin kasar Remo inda Osinbajo ya fito, ya ce mataimakin shugaban Najeriyar ya san abin da ya fi dacewa da shi a 2023.

'Yan 'Act Now' su na kamfe

Mai martaba ya yi wannan kiran ne a lokacin da wasu matasa a karkashin tafiyar ‘Act Now’ suka ziyarci Sarkin a fadarsa a garin Sagamu a farkon makon nan.

Wadannan matasa su na goyon bayan Yemi Osinbajo ya nemi takarar shugaban kasa a 2023.

Sarkin Yarbawa
Babatunde Ajayi da 'Yan Act Now Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Osinbajo ya cancanta

Babban Sarkin ya yabi Osibanjo, ya ce jagora ne wanda ya san abin da ya kamata, ya kuma bayyana cewa zai gyara kasar nan idan shugabanci ya zo hannunsa.

Sarki Babatunde Ajayi ya ce Najeriya ta na cikin matsala, don haka ake bukatar jagoranci na kwarai. Jaridar nan ta Tribune ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

A cewar Basaraken wani abokinsa ya fada masa kwanan nan cewa idan babu ranar da Najeriya za ta gyaru, to shi ne a ga Osinbajo bai shiga takara a zaben 2023 ba.

“Akwai abubuwa da yawa da za ayi. Ina mai tabbatar maku da cewa Farfesa ya san abin da ya dace da kasar nan, ya san abin da ya dace da shi da kuma iyalinsa.”
“Zabi ne na mutum, ina fatan in samu dama in zauna da shi, sai in tambaye sa ‘me kake shirin yi?’ ana damu na da yawan tambaya ta; ‘za ka yi takara ko ba za kayi ba?’
“Na tabbata zai bani amsa kai-tsaye.” - Oba Babatunde Ajayi

Zaben shugabannin APC

A makon nan ne ake ji cewa jam’iyyar APC ta sa Gwamnonin jihohi da manyan Ministoci masu-ci a kwamitocin da za su shirya babban zaben shugabanni na kasa.

Akwai irinsu Farfesa Babagana U. Zulum, Inuwa Yahaya, Femi Fani-Kayode a kwamitocin da su taimaka wajen gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tsohon Mai ba APC shawara ya cire Tinubu, Osinbajo daga lissafin 2023 saboda abu 2

Asali: Legit.ng

Online view pixel