Gwamnoni, Ministoci da kusoshi 20 da za su jagoranci zaben APC da za a shirya a 2022

Gwamnoni, Ministoci da kusoshi 20 da za su jagoranci zaben APC da za a shirya a 2022

  • APC ta kafa kananan kwamitoci 20 da za su taimaka mata wajen shirya zaben shugabanni da za ayi
  • A ranar 26 ga watan Maris 2022 Jam’iyyar APC mai mulki za ta zabi shugabanninta na kasa a NWC
  • Sanata John James Akpanudoedehe ya fitar da sanarwa a kan yadda aka kafa kananan kwamitoci

Jaridar Daily Trust ta ce APC ta bada wannan sanarwa ne a wata takarda da ta fitar ta hannun sakataren rikon kwarya na kasa, John James Akpanudoedehe.

Ministoci da gwamnonin jihohi da manyan ‘yan siyasa za su jagoranci wadannan kwamitocin da APC ta ba alhakin gudanar da zaben shugabanninta na kasa.

A cikin kwamitocin akwai na tsare-tsare, bada gudumuwa, tantance ‘yan takara, shigar da korafi, gudanar da zabe, samar da masauki, karan zabe, da sauransu.

Kara karanta wannan

Siyasar 2023: Atiku, Tinubu da sauran ‘Yan takara za su san matsayarsu nan da kwana 92

Sauran kwamitocin kamar yadda rahoton ya bayyana sun hada da na shakatawa, tsaro, zirga-zirga. Akwai kwamitocin kudi, kasafi, masu sa ido da kula da lafiya.

Vanguard ta kawo karin bayanin yadda aka raba wadannan kwamitocin da za a rantsar a Abuja.

Yadda aka yi kason

Babban kwamitin tsare-tsare yana da mutane 12, yayin da kwamitn gudumuwa yake da mutum bakwai. Sauran kwamitocin kuma duk sun kunshi mutane 40 ne.

Mai Mala Buni
Shugaban kasa tare da Shugaban APC Hoto: BBC ; Daga @BBCNewsHausa
Asali: Facebook

Kwamitin tantance ‘yan takara zai kasance karkashin gwamnan Kwara, Alhaji Abdulrahaman Abdulrazaq da Emmanuel Chikwu Emeka a matsayin sakatarensa.

Kwamitocin zabe da na korafin zabe su na karkashin Dapo Abiodun da Aminu Bello Masari. David Umahi da Simon Lalong za su kula da kyale-kyale, sufuri da zirga-zirga.

FFK ya samu kujera

Kara karanta wannan

Borno: Mayakan ta'addancin ISWAP sun sheke rayuka 5 Kautikari a sabon hari

Babajide Sanwo-Olu da Femi Fani Kayode sune shugabannin kwamitin yada labarai. Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello aka ba nauyin kula da kwamitin tsaro.

Abubakar Malami shi ne shugaban kwamitin shari’a. Gwamnan Zamfara zai rike kwamitin samar da masauki. Gwamna Inuwa Yahaya ne zai kula da sha’anin kasafi.

Gwamnan Imo, Hope Uzodinma ne zai jagoranci kwamitin da zai saurari korafi tare da Barr. Shuaibu Aruwa SAN. Babagana Zulum ya samu rikon wani kwamiti daga cikinsu.

Shugaban kwamitin kudi shi ne Badaru Aubakar. Sauran shugabannin kwamitocin sun hada da Ben Ayade, Hon. Ahmed Idris Wase, Kashifu Inuwa, da Geoffery Onyeama.

Manya za su rasa mukamansu

Ku na da labari cewa masu rike da mukaman gwamnati za su yi murabus tun da har Muhammadu Buhari ya rattaba hannunsa a kudirin gyaran zaben Najeriya.

Dokar kasa ta yi tanadi duk mai neman kujerar siyasa, zai ajiye mukamin gwamnati kafin zabe. Hakan na nufin Ministoci da sauran shugabannin MDA za su rasa mukami.

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

Asali: Legit.ng

Online view pixel