Abin da mutane suke fada yayin da Kwankwaso suka kirkiro sabuwar tafiya daf da 2023

Abin da mutane suke fada yayin da Kwankwaso suka kirkiro sabuwar tafiya daf da 2023

  • A yau ne Rabiu Musa Kwankwaso da wasu ‘yan siyasan Najeriya su ka kaddamar da tafiyar TNM
  • Mutane su na ta tofa albarkacin bakinsu a game da wannan matakin da ‘yan siyasar suka dauka
  • Wasu su na ganin burinsu Kwankwaso ba zai bulle ba, wasu kuma na ganin hakan ne ya kamata

Abuja - Legit.ng Hausa ta tattaro ra’ayin wasu daga cikin masu bibiyar shafukan sada zumunta a game da kungiyar The National Movement da aka kafa a Abuja.

Ga abin da wasu suke fada a shafin Twitter:

Kwankwaso ya tafka babbar caca. Amma dama haka siyasa ta gada.

- Dr Nasir Daniya

Kwankwaso ya yi kuskure a 2015, kuma har yanzu yana da-na-sani. Babu yadda za ayi ya cin ma burinsa ko wace jam’iyya zai shiga kuma yanzu. Ya yi kuskuren da zai ta bin shi.

- Jabir Ishaq

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba na tunanin Kwankwaso zai farfado daga kataborar da ya yi bayan 2015. Shekaru sun fara tafiya, kuma ya kinkimo gwargwamayar da ba za ta je ko ina ba.

- Adamu Hayatu

Kwankwaso zai yi da-na-sanin kafa sabuwar jam’iyya, jam’iyyu biyu kadai za su iya tasiri a Najeriya.

- Bulama

Da tarin kwarewarsa a iyasa, ina mamakin yadda Kwankwaso ya kirkiro jam’iyya bayan lokaci ya kure. Lokaci ba zai isa har ya ratsa ko da daya bisa ukun kasar nan ba ne.

- Kabir Mukhtar

Sanata Kwankwaso ya kinkimo abokan Tinubu a siyasa na 1999 a sabuwar jam’iyyarsa. Mafi yawancinsu ba su da abin yi tsawon shekaru 15 da suka wuce.

- Real Aghedo

Kuskuren farko da kataborar da ya yi shi ne wajen kafa tafiyar Kwankwasiyya. Mabiyansa sun fi karkata ga Kwankwasiyya a kan wata jam’iyyar siyasa.

- Ahmad AIG

Kwankwaso a ICC
Kwankwaso a taron TNM Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Kwankwaso sun yi daidai

Wannan mutumi zai iya zama shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa a duk jam’iyyar da yake so, a maimakon haka zai ya zabi kafar da za ta ba mutane damar yin zabi ga kasarsu. Ya zabi ya nesanta kansa daga hadamammun da suka ruguza kasar nan.

- Sameer Lukman

Idan ka fahimci su wanene ke da ta-cewa a siyasa, za ka san cewa hanyar da Kwankwaso ya dauka ta na cikin mafi kyawun dabarar siyasa da aka yi a yanzu.

- Omar Wambai

Tafiyar Kwankwaso za ta batawa bara-gurbin ‘yan takara lissafi a zaben 2023.

- Aminu Shanono

PDP ta na bukatar Kwankwaso. Bai dace ka na yi wa irin APC adawa ba, kuma ka na rasa manyan kusoshinka.

- Novie Everest

Martanin wasu ‘Yan Facebook

Kawai Kwankwaso suje su tallatawa Tinubu, da an mai wulakanci a Congress ya tarwatsa APC ya tattaro structure dinshi ya dawo a buga.

- Abdul Haleem Ringim

"Manufar TNM shine bawa manyan jam'iyyun kasar nan APC da PDP tsoro wajen yin gangami domin nunawa jam'iyyun cewa ga wasu gungun mutane can zasu samar da third force , wanda a tunanin masu gangamin su jam'iyyun zasu tsorata da wannan gangamin har takai ga sun nemesu, idan suka nemesu su kuma sai su gindaya musu sharadudduka na buqatarsu acikin jam'iyyar idan ta amince sai su narke aciki
Idan kuma jam'iyyun basu miqa qoqon bararsu ba da kuma samun daidaito to wannan gangami zasu qirqiri jam'iyya ko kuma su dakko wata a cikin kananun jam'iyyu
Idan har daga cikin manyan jam'iyyun nan suka nemi wannan gangami kuma suka samu daidaito to gangamin yayi nasara
Idan kuma gangamin yasamu tasgaro na gayyata daga cikin wadannan manyan jam'iyyun to tabbas ansamu faduwa kuma da yawa daga cikin wasu yan siyasar sun halaka kenan a siyasa

Ita dai wannan harka, harka ce wanda idan an dace an rayu akasin haka kuma an mutu kenan a siyasance."

- Aminu Dumbulum

Ni Kwankwaso nake yi ba Jam'iyya ba. Sunan kwankwasiyya ya fi karfi akan duk wata jam'iyya da take Kano. Shi yasa duk inda kwankwa ya shiga shi yake zama mai fada aji don ya kafa sunansa sama da jam'iyyar da zai shiga.
Mafi yawancin mutane sun fi son mayaudara in ana maganar siyasa da mu'amala. Shi kuma Kwankwaso baya yaudara kuma baya juyawa talaka baya. Duk wani hasashe na siyasa da kwankwaso zai yi akan talaka yake yinsa. Wannan ina da yakini akan hakan.
Duk inda kwankwaso zai shiga ina tare dashi a siyasa 100%. Shi kadai ne ya bani yakini akan za'a iya samar da siyasar ci gaba a Arewa da Nigeria gaba daya.

- Mahmud Galandaci

An yankewa TNM cibiya

Dazu kun ji cewa tsohon gwamnan na jihar Kano shi ne gaba wajen wannan tafiya da ake tunanin za ta rikida ta zama jam’iyya a zaben shugaban kas ana 2023.

Wadanda suke tare da Kwankwaso a TNM sun hada da Murtala Nyako, Lukcy Igbinedion, Achike Udenwa, Buba Galadima, Farfesa Rufai Alkali da su Sanata Rufai Hanga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel