Abubuwa 10 da Kwankwaso ya fada wajen kaddamar da sabuwar tafiyar siyasarsu

Abubuwa 10 da Kwankwaso ya fada wajen kaddamar da sabuwar tafiyar siyasarsu

  • A ranar Talata 22 ga watan Fubrairu 2022, Rabiu Musa Kwankwaso da wasu ire-irensa suka kaddamar da tafiyar TNM
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano shi ne gaba wajen wannan tafiya da ake tunanin za ta rikida ta zama jam’iyya a zaben 2023
  • Wadanda suke tare da Kwankwaso a TNM sun hada da Murtala Nyako, Lukcy Igbinedion, Achike Udenwa da Rufai Hanga

Abuja - Legit.ng Hausa ta kawo muhimman jawaban da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wajen yankewa wannan tafiya cibiya a dakin taro na ICC.

Tsohon Ministan tsaron na Najeriya ya fitar da jawabin na sa a shafinsa na Twitter dazu.

1. Bari in fara da yi maku maraba zuwa wajen wannan taro na dabam mai tarihi da ya tattaro mutane daga kusa da nesa – yara da manya – maza da mata da nufin sake gyara kasarmu. Ina godiya da ku ka samu lokaci, ku ka halarci wannan taro.

Kara karanta wannan

Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

2. Mun zabi ranar yau ta musamman 2/22/2022 domin tattaro mutane daga wurare, jam’iyyu, addinai, da kabilu dabam-dabam domin kaddamar da wannan gagarumar tafiyar siyasa da za ta canza akalar kasarmu, ta kuma ceto mu daga ha’ula’i.

3. An fara wannan tafiya ne a kakar 2021 lokacin ana fama da annobar COVID-19. Mun fara zama a karkashin lemar ‘Abokan Kwankwaso’ domin a nemawa Najeriya mafita. Mu na yi wa kanmu kallon jagorori bayan zamanmu ‘yan siyasa.

Mu na da jama'a daga ko ina

4. A haka aka haifo wannan tafiya ta fadin kasar nan kamar yadda ku ke ganin an samu mutane daga ko ina a Najeriya da ketare. Mun ajiye siyasa, mun gayyaci jama’a daga kowace jam’iyya. Dole mu kaucewa layin jam’iyyun da ake da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

5. Mu na da mabiya a kowace mazaba a karamar hukuma da ke Najeriya Manufar wannan tafiya ita ce samar da kasa mai ‘yanci, adalci da dama ga al’umma domin a cin ma burin rayuwa. Abin da muka sa gaba su ne amana, gaskiya, kishin kasa, dsr.

Kara karanta wannan

Sakamakon zirga-zirgar Buhari: Kasar Ingila ta narka Naira Biliyan 5 domin inganta wuta

Tafiyar TNM
Bikin kaddamar da TNM Hoto: @BBCNewsHausa
Asali: Facebook

Matsalar rashin tsaro

6. Ana cikin fagamniya a dalilin matsalolin garkuwa da mutane, IPOB, Boko Haram da sauran masu tada zaune-tsaye da shugabanni suka gagara shawo kansu. A shirye muke, mu yi maganin wadannan kalubale ba da karfin bindiga kawai ba.

7. TNM ta san da zaman masu kiran a barka Najeriya, da masu neman a sauya fasalin kasa ko a canza tsari. Duk za mu saurari kowa da nufin inganta rayuwar al’umma. Akwai bukatar a yi gyara a yadda ake kason dukiyar kasa a tsarin mulki.

A ba mutane muhimmanci

8. Ba a samun cigaba a Duniyar yau sai da ilmi da gina ‘Dan Adam. Tafiyar TNM za ta maida hankali wajen raya al’umma tare da adalci da ba kowa dama. Domin samar da ayyukan yi, ya wajaba a samar da abubuwan more rayuwa, a gyara masana’antu.

9. Za mu yi taka-tsan-tsan da dukiyar kasa, mu yi abin da ya kamata a game da bashin da ake bin mu. Mu na kuma kira ga al’umma su taya mu kokari wajen tabbatar da zabe mai nagarta tare da ba bangaren shari’a da majalisa cin gashin kansu.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU za ta yi zaman farko da Gwamnatin Tarayya mako 1 da fara yin yajin-aiki

10. Ina kira ga dinbin jama’a; ‘yan kwadago, matasa, malamai, manoma da kwararru duk su tashi domin a gyara kasa da su. Mu na yin kira ga mutane su daina zama a gefe su na kokawa da halin da ake ciki, dole mu tashi tsaye domin mu ceci kasar mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel