'Yan siyasa 4 da su ka rike Minista a mulkin Jonathan, yanzu su ne Gwamnonin jihohinsu

'Yan siyasa 4 da su ka rike Minista a mulkin Jonathan, yanzu su ne Gwamnonin jihohinsu

  • Akwai wasu daga cikin Ministocin Najeriya da suka yi murabus, suka nemi takarar gwamna a zaben 2015
  • Wasu daga cikinsu sun yi nasara, amma irinsu Labaran Maku da Musliu Obankiro ba su kai labari ba
  • A wancan lokaci Goodluck Ebele Jonathan ne Shugaban kasa, shi karon kasa ya nemi ya zarce a mulki

Legit.ng Hausa ta kawo Ministocin gwamnatin Dr. Goodluck Jonathan da yanzu Gwamnoni ne a kasar nan:

1. Nyesom Wike

Nyesom Wike ya fara rike kujerar karamin Ministan ilmi a gwamnatin tarayya a 2011. A 2013 ne Wike ya zama babban Minista na ilmi bayan an sallami Farfesa Ruqayyah Rufai.

Wike ya sauka daga mukaminsa, ya nemi takarar gwamnan Ribas a jam’iyyar PDP. ‘Dan siyasar ya doke ‘yan takarar tsohon uban gidansa, Rotimi Amaechi a zabukan 2015 da 2019.

Kara karanta wannan

Karya ta kare: Abin da mutane ke cewa da NDLEA ta zargi Abba Kyari da safarar kwayoyi

2. Samuel Ortom

A shekarar 2011 aka nada Samuel Ortom a matsayin Ministan masana’antu da kasuwanci na Najeriya. Haka zalika ya lura da ma’aikatar jiragen sama bayan an tsige Stella Oduah.

Samuel Ortom ya na cikin Ministocin da suka ajiye aikinsu, suka tafi takarar gwamna. Ortom ya lashe zaben gwamnan Benuwai a APC, daga baya ya koma PDP har ya samu tazarce.

'Yan siyasa
Nyesom Wike, Darius, Bala Mohammed da Ortom Hoto; The Guardian/Daily Post/Channels/Freedom Radio
Asali: UGC

3. Darius Ishaku

Arch. Darius Dickson Ishaku ya rike Ministan harkokin Neja-Delta a gwamnatin Goodluck Jonathan. An kuma yi lokacin da ya kula da ma’aikatun lantarki da na muhalli.

Gabanin zaben 2015 ne Darius Ishaku ya sauka daga kujerar Minista ya nemi tikitin PDP a zaben gwamnan Taraba, ya samu. Haka kuma ya lashe zaben zama gwamna na jihar.

Bayan ya yi nasara a zaben, Ishaku ya yi ta shari’a da ‘Yar takarar APC, Aisha Jummai Alhassan a kotu. A 2019 ne Ishaku ya zarce a kan mulki, ya ba APC ratar kuri’u 150, 000.

Kara karanta wannan

Guguwar sauya sheka: Ana gab da yiwa APC mai kankat gabannin 2023 - Tambuwal

4. Bala Mohammed

Na karshe a jerin na mu shi ne gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed. Sanata Bala yana cikin Ministocin tarayyan da aka nada a watan Yulin 2011 a Najeriya.

A zaben 2015 ne tsohon Ministan na birnin tarayya Abuja ya yi nasarar zama gwamnan Bauchi a karkashin PDP. Sanata Bala Mohammed ya kifar da APC da ke mulki a jihar.

Meyasa PDP ta fadi zaben 2015?

Goodluck Jonathan ya sha kasa a takarar shugaban kasa a karon farko a tarihin Najeriya, an ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana silar rashin nasarar PDP a 2015.

Kwankwaso ya ce Jonathan bai san su wanene 'yan siyasar da za su taimaka masa ya ci zabe, sannan ya na ganin PDP ba ta kama hanyar samun nasara a zaben 2019 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel