Jagororin Kwankwasiyya sun juyawa Kwankwaso baya, ana kishin-kishin za su tsallaka APC

Jagororin Kwankwasiyya sun juyawa Kwankwaso baya, ana kishin-kishin za su tsallaka APC

  • Tsohon kwamishinan ayyuka a Kano, Mu’az Magaji ya ce tsagin G7 zai tarbi wasu manyan ‘yan adawa
  • Mu’az Magaji ya ce akwai wasu jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da za su tsallako bangarensu
  • Daga cikin wadanda ya ce za su dawo APC akwai Yunusa Dangwani, Madakin-Gini da Danburam

Kano - Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Mu’az Magaji wanda aka fi sani da ‘Dansarauniya, ya kyankyasa samun wasu sababbin shiga cikin APC.

Injiniya Mu’az Magaji ya fito shafinsa na Facebook a ranar Juma’ar da ta wuce ya na cewa wasu jagororin bangaren Kwankwasiyya, su na shirin shigowa jam’iyyar APC.

Magaji ya ce tsaginsu na G7 zai kara yawa a yayin da suke sauraron shigowar wasu manyan ‘yan adawa. 'Yan G7 su na karkashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau.

Daga cikin wadanda za su tsallako zuwa bangaren G7 a cewar tsohon kwamishinan akwai Dr. Yunusa Dangwani, Aliyu Madakin Gini, da kuma Dr. Yusuf Danbatta.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kashe Buba Danfulani da kwamandojin ISWAP 4 a Sambisa

Sai Hon. Nuhu Danburam, Umar Kuliya, Aminu Dala, Zainab Abdu Bako. Akwai su Garba Diso, Sani Rogo, Abdullah Ajiya da wasu da Kwankwasiyya ta ke ji da su.

Jagororin Kwankwasiyya
Wani taro da Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranta Hoto: Hon. Saifullahi Online TV
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda ake rade-radin za su koma bangaren ‘Yan taware a APC sun hada da tsofaffin kwamishinoni, tsofaffin ‘yan majalisa da hadiman Sanata Kwankwaso.

Rahotannin da mu ka samu shi ne a ranar Asabar ne Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci taro na masu hannu-da-shuni a jam’iyyar PDP a fadin jihar Kano.

Wadannan mutane da aka saba gani a gefensa a wajen irin wannan taro duk ba su samu halarta ba.

Taron PDP a Kano

An yi wannan zama babu irinsu Yunusa Adamu Dangwani, Aliyu Sani Madaki, Aminu Dala, Zainab Audu Bako, Yusuf Bello Danbatta, da Abubakar Nuhu Danburam.

Wata majiya ta ce wadannan manyan ‘yan siyaa sun yi watsi da taron da Kwankwaso ya kira, sun je wajen bikin saukar Al-Kur’anin diyar Hajiya Zainab Audu Bako.

Kara karanta wannan

'Yan siyasa 4 da su ka rike Minista a mulkin Jonathan, yanzu su ne Gwamnonin jihohinsu

Kwankwaso ya caccaki PDP da APC

A karshen makon da ya gabata ne ku ka ji labari cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya kyankyasa inda ya sa gaba a siyasa, inda ya yi wa PDP da kumaAPC kaca-kaca.

A wata hira da aka yi da Kwankwaso, ya soki salon tafiyar jam’iyyarsa ta PDP da APC, ya ce dukkaninsu ba su da abin da za su iya nunawa al'umma a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel