Sukar Da Ortom Ke Yi Wa Buhari Ba Ya Nufin Ya ƙi Jininsa, Hadiminsa

Sukar Da Ortom Ke Yi Wa Buhari Ba Ya Nufin Ya ƙi Jininsa, Hadiminsa

  • Nathaniel Ikyur, Sakataren watsa labarai na Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ya ce sukar da mai gidansa ke yi wa Buhari ba ya nufin baya son shugaban kasar
  • Ikyur, yayin wani jawabi da ya yi a Abuja ya ce Ortom yana sukar wasu tsare-tsaren gwamnatin Buhari ne domin yana son ya taimaka masa ya bar tarihi na gari
  • Hakazalika, Ikyur ya kara da cewa babu wanda ke tsammanin Gwamna Ortom zai zuba ido ana kashe mutanensa babu dare ba rana ba zai yi magana don kwato musu hakkinsu ba

FCT, Abuja - Nathaniel Ikyur, babban sakataren watsa labarai na Samuel Ortom, gwamnan Jihar Benue, ya ce mai gidansa bai tsani Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Kara karanta wannan

Ba 'yan IPOB ne ke son ganin bayan ka ba: Adamu Garba ya yi martani ga Abba Kyari

Da ya jawabi a ranar Juma'a wurin wani taro a Abuja, a cewar rahoton The Cable, Ikyur ya ce Ortom yana son ya taimaka wa Buhari ya bar tarihi mai kyau ne.

Sukar Da Ortom Ke Yi Wa Buhari Ba Ya Nufin Ya ƙi Jininsa, Hadiminsa
Ortom bai tsani Buhari ba, taimakonsa ya ke yi, Hadimin Gwamna. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ortom ya kasance cikin masu yawan sukar salon mulkin Buhari, musamman a bangaren tsaro da ya shafi yankuna a kasar, musamman jiharsa.

Da ya ke tsokaci kan kalaman gwamnan, babban sakataren watsa labaran ya ce ba a tsamanin Ortom ya yi shiru kan hare-haren da aka kai wa a garuruwa a Benue.

Ya ce:

"Ina son jadada cewa mai gida na, Gwamna Samuel Ortom, bai tsani Shugaba Buhari ba. Kalamansa kan halin da kasa ke ciki da irin salon mulkin shugaban kasar ba ya nufin ya ki jininsa."
"Ba bu mutum mai hankali da zai zuba ido a yayin da ake kashe mutanensa a kowanne rana. Na san kana da masaniya kan kashe-kashen da makiyaya ke yi a Logo, Guma, Agatu da wasu sassan Benue.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Minista ya yi martani kan tafiyar ASUU yajin aiki, za a biya musu bukata

"Kana zaton gwamnan ya yi shiru ne? Zai cigaba da yin magana tare da yin tsayin daka saboda mutanensa."

Ortom yana sane da kirar da ake masa na fitowa takarar Sanata

Ikyur ya kara da cewa ana neman Ortomya fito ya nemi takarar Sanata amma yana addu'o'i kafin ya yanke shawara, rahoton The Cable.

"Gwamna Ortom ya san kiraye-kirayen da wasu ke masa na neman ya fito takarar Sanata a 2023, amma kamar yadda ya saba, sai ya yi addu'a kafin ya bayyana matsayarsa nan gaba," in ji Ikyur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel