Rikicin Kano: Sanata Shekarau ya caccaki Ganduje da APC, yace yanzu aka fara

Rikicin Kano: Sanata Shekarau ya caccaki Ganduje da APC, yace yanzu aka fara

  • Sanata Ibrahim Shekarau ya maida martani kan baiwa tsagin Ganduje takardar shedar zama shugabannin APC a Kano
  • Tsohon gwamnan yace kalaman da Ganduje ya yi bayan hukuncin kotu bai dace da matsayinsa na shugaban al'umma ba
  • A jiya alhamis ne, Kotun ɗaukaka kara ta soke hukuncin babbar kotun tarayya, wacce ta baiwa tsagin Shekarau gaskiya

Kano. - Sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya nuna rashin jin daɗinsa da kalaman gwamna Ganduje na murnar samun nasara a Kotu ranar Alhamis.

Premium Times ta rahoto cewa Shekarau ya zargi Ganduje da yin kalaman batanci ga mambobin tsaginsa a jawabinsa bayan hukuncin Kotu.

Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin babbar Kotun tarayya dake Abuja, wanda ya baiwa shugabannin APC na tsagin shekarau nasara.

Rikicin APC a Kano
Rikicin Kano: Sanata Shekarau ya caccaki Ganduje da APC, yace yanzu aka fara Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A ranar Alhamis, Kotun ta yanke cewa ƙaramar Kotun ba ta da hurumin shiga shirgin matsalar cikin gida ta wata jam'iyyar siyasa.

Kara karanta wannan

Murna ta ɓarke a APC tsagin Ganduje bayan sun lallasa su Shekarau a kotun ɗaukaka ƙara

Hukuncin ya sake maida jagorancin tafiyar jam'iyyar APC reshen Kano hannun tsagin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Uwar jam'iyya ba ta mana adalci ba - Shekarau

A wata fira da BBC Hausa, Shekarau ya bayyana cewa APC ta ƙasa ba ta yi musu adalci ba, kuma abun ya yi matuƙar ba su mamaki.

Sanatan ya ce:

"Ba kowane mutum ne idan bai samu abin da yake so ba zai ji rashin daɗi mun karɓi kaddara daga Allah kuma muna fatan ya zama alkairi a wajen mu. Mun ji hukunci, zamu tattauna da lauyoyin mu."
"Wani rashin adalci shi ne wata biyu muna da hukuncin Kotu a hannun mu, muka ce a rantsar da shugabannin mu a ba su shaidar zaɓe, albashi kuma a rike har sai an je kotun Koli amma suka ce a zauna sulhu."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: APC a Kano: Tsagin Shekarau ya maida martani kan nasarar gwamna Ganduje a Kotu

"Amma abun mamaki ko awanni biyu ba'a yi da yanke hukunci ba uwar jam'iyya ta kira su, ta baiwa shugaba takardar sheda cewa shine zaɓaɓɓen ciyaman."

Shin ya tsagin Shekarau ke ganin APC ta ƙasa?

Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa a baya sashin shari'a na uwar jam'iyya ta ƙasa ya bada shawarar a rantsar da tsagin su amma suka ƙi.

"Ba'a mana adalci ba, a bayan sai da aka baiwa shugaban APC shawara amma ya yi kunnen uwar shegu. A zahirin gaskiya ba'a mana adalci ba.

A wani labarin kuma Matashin dan takarar shugaban ƙasa a 2023 ya gana da IBB, ya nemi ya sa masa albarka

Adamu Musa, ɗan shekara 40 a duniya dake neman gaje kujerar Buhari ya kai wa tsohon shugaban ƙasa ziyara a Minna, jihar Neja.

Matashin ya ce ya gana da Ibrahim Badamasi Babangida ne domin neman albarka, da kuma goyon bayansa a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da nasarar tsagin Shekarau, Ganduje ya samu nasara

Asali: Legit.ng

Online view pixel