Bayan shekaru 23 tare, tsohon Gwamnan APC ya raba jiha da Uban gidansa Bola Tinubu

Bayan shekaru 23 tare, tsohon Gwamnan APC ya raba jiha da Uban gidansa Bola Tinubu

  • A halin yanzu an raba jiha tsakanin Rauf Aregbesola da kuma Mai gidansa, Asiwaju Bola Tinubu
  • Rauf Aregbesola ya rike kujerar Kwamishina daga 1999 zuwa 2006 a Gwamnatin Bola Tinubu a Legas
  • Ministan ya yi wa Tinubu da Gwamna Oyetola kaca-kaca, ya na tare da Adeoti a zaben jihar Osun

Osun - Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya nuna cewa dangantakarsa a siyasa da jagoransa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta kare.

PM News ta ce Rauf Aregbesola ya fito gaban Duniya ya bayyana cewa ba ya goyon-bayan Gwamna Gboyega Oyetola wanda yake tare da Bola Tinubu.

An dade ba a samun jituwa tsakanin bangaren Ministan harkokin cikin gidan kuma tsohon gwamnan jihar Osun da tsagin magajinsa, Gboyega Oyetola.

Moshood Adeoti ne Gwamnan gobe?

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya yi magana a kan takarar Tinubu da Osinbajo a zaben Shugaban kasa

Rauf Aregbesola ya bayyana cewa ba zai marawa Gwamna Oyetola baya a zaben fitar da gwani da za ayi ba, ya ce su na tare da Moshood Adeoti a zaben APC.

Alhaji Adeoti ya rike Sakataren gwamnati a Osun, yana cikin manyan na-kusa da Aregbesola. Shi kuma Gwamna mai-ci ‘danuwa ne ga Asiwaju Bola Tinubu.

The Cable ta ce tsohon gwamnan ya yi kaca-kaca da gwamnatin Gboyega Oyetola wanda ya ce ta saki layin da jam’iyyarsu ta APC mai mulki ta dauko a jihar.

Bola Tinubu
Rauf Aregbesola da Bola Tinubu Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Da yake magana da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a Ijebu Ijesa, Rauf Aregbesola ya sha alwashin cewa Moshood Adeoti zai samu tikitin APC, kuma ya lashe zaben 2022.

Asiwaju Tinubu v Rauf Aregbesola

Nan da kwanaki hudu ake sa ran APC za ta shirya zaben fitar da gwani na ‘dan takarar gwamna a Osun. Alamu na nuna bangarorin biyu za su goge raini a zaben.

Kara karanta wannan

Karya ta kare: Abin da mutane ke cewa da NDLEA ta zargi Abba Kyari da safarar kwayoyi

Kamar yadda aka ji a wani bidiyo, Aregbesola ya soki Tinubu, ya ce ya bada goyon-baya a hana Akinwumi Ambode tazarce, amma yana marawa Oyetola baya.

Ministan ya kuma jaddada cewa bangaren Rasaq Salinsile ne ainihin shugabannin APC a jihar Osun. A cewarsa, su za su ba jam’iyyar APC nasara a zaben bana.

Zaben 2023

A makon nan ne aka ji cewa wadanda tsofaffin Sojojin kasar nan ke marawa baya a zaben shugaban kasa duk sun fito ne daga bangaren Kudancin Najeriya.

Cif Olusegun Obasajo yana so tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ko waninsa ya tsaya takara, sai Attahiru Jega ya zama mataimakin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel