Gwamnan APC ya yi magana a kan takarar Tinubu da Osinbajo a zaben Shugaban kasa

Gwamnan APC ya yi magana a kan takarar Tinubu da Osinbajo a zaben Shugaban kasa

  • Ben Ayade ya na ganin Bola Ahmed Tinubu ya cancanci ya nemi takarar kujerar shugaban Najeriya
  • Farfesa Ayade ya ce Bola Tinubu ya yi duk wahalar da za a iya, don haka babu laifi idan ya na son takara
  • Gwamnan na jihar Kuros Riba ya kuma ba Farfesa Yemi Osinbajo shawarar ya jarraba sa’arsa a zaben 2023

Cross River - Gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade ya ce babban jagoran APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya na da damar da zai nemi kujerar shugaban kasa.

BBC tayi hira da Farfesa Ben Ayade inda aka ji yana cewa la’akari da wahalar da Bola Ahmed Tinubu ya sha da APC, babu laifi don ya fito ya bayyana muradinsa.

Kara karanta wannan

Abin da Jonathan ya fada mani game da tsayawarsa takara a 2023 - Gwamnan Bauchi

Farfesa Ayade ya ce tsohon gwamna Tinubu ya yi yaki wajen ganin gwamnatin Muhammadu Buhari ta kafu, aka kifar da PDP shekaru kimanin bakwai da suka ce.

A cewar Gwamna Ayade, muddin jam’iyyar APC ta ce a marawa Bola Tinubu baya, zai goyi bayan sa tun da ya yi bauta, ba zai yiwu ayi masa dare a zabe mai zuwa ba.

“Duk wanda zai fito takara daga yankin kudancin Najeriya, ya fito. Za ma a samu karin wadanda za su nemi takara.”
“Idan ka tambaye ni game da Bola Tinubu, zan ce ya yi daidai da ya fito takara, dalili kuwa shi ne ya yi wa Buhari kokari."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fadar Shugaban kasa
Shugaban kasa Buhari da Gwamna Ayade Hoto: Femi Adesina Daga: Twitter
Asali: Twitter
“Ya yi yaki wajen ganin an kafa gwamnatin nan. Wanda ya yi wannan kokari zai ga cewa lokaci ya yi da zai karbi mulki.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shettima ya bayyana abun da arewa ba za ta iya yiwa Tinubu ba

“Ba zan iya cewa ya yi daidai da ya fito ba. Amma ina cikin 'ya 'yan jam’iyya, APC za ta auna shi da sauran ‘yan Kudu.”
“Ba za ta yiwu ya gama shan wahala da jam’iyyar APC ba, sai kuma yanzu a ce ba a bukatarsa saboda ya tsufa.”

- Ben Ayade

Takarar Osinbajo

Ayade ya ce Yemi Osinbajo zai iya jarraba sa’arsa domin ya yi aiki da Shugaban kasa na shekaru takwas, Buhari ya san shi sosai, kuma kusan shi zai zabi magajinsa.

Gwamnan na APC ya ce idan Farfesa Osinbajo aka zakulo a matsayin wanda zai yi takarar shugaban kasa, babu abin da ya rage masa sai ya bada goyon baya.

Mulki ya koma Kudu

Mai girma Ben Ayade ya bayyana cewa yana tare da gwamnonin kudancin Najeriya da ke da ra’ayin cewa bai dace mulki ya sake komawa Arewa a bayan 2023 ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Bayyana Wanda Zai Zaba Wa APC Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023

Baya ga haka, gwamnan na Kuros Riba ya ce zai mara baya duk wanda jam’iyyarsa ta APC mai mulki ta tsaida a takarar shugaban kasa, muddin daga yankin ya fito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel