Abin da Jonathan ya fada mani game da tsayawarsa takara a 2023 - Gwamnan Bauchi

Abin da Jonathan ya fada mani game da tsayawarsa takara a 2023 - Gwamnan Bauchi

  • Gwamnan jihar Bauchi ya yi magana a kan takarar Shugabancin kasa da ya sa gaba a zaben 2023
  • Sanata Bala Abdulqadir Muhammad ya yi zama na musamman da Dr. Gooduck Jonathan a Abuja
  • Mai girma gwamnan ya bayyana cewa idan tsohon shugaba Jonathan zai yi takara, shi zai hakura

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulqadir Muhammad ya ce yana da duk abin da ake bukata wajen neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Leadership ta ce Bala Abdulqadir Muhammad ya ce zai iya kalubalantar kowa a filin zabe face mai gidansa, Dr. Goodluck Jonathan, idan zai sake yin takara.

Gwamnan na jihar Bauchi ya yi wannan magana ne bayan wata ganawa da ya yi da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a gidansa a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

Bala yake cewa Jonathan ya ba shi shawara cewa ka da ya janye burinsa na neman kujerar shugaban kasa domin shi karon kansa zai iya fitowa takarar.

“Sai na fada masa cewa idan har zai fito takarar shugaban kasa, ba zan kalubalance shi bai dan shi ma zai nemi mulki, ba zan yi fito-na-fito da shi (Jonathan) ba.”
“A matsayina na yaronsa mai ladabi, ba zan janye daga neman wannan mukami ba.”
Gwamnan Bauchi
Bala Mohammed da Goodluck Jonathan Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

“Na fada masa idan zai yi takara, ba zan yi ba, ko da a wata jam’iyya ce da ba APC ko PDP ba. Kasar nan ba za ta bar ni in yi takara idan shi ma zai yi ba.”

Bala zai nemi takara a 2023

Jaridar Leadership ta ce kwanakin baya aka aji gwamnan Bauchi yana cewa akwai yiwuwar ya tsaya neman shugabancin Najeriya a zaben shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Dalilai 2 da suka sa Farfesa Osinbajo ba zai yi takara da Bola Tinubu ba - Jigon APC

A cewar Sanata Bala Abdulqadir Mohammed, bai jin tsoron wani ‘dan takarar shugaban kasa, har da irinsu Alhaji Atiku Abubakar wanda ya fito daga yankinsa.

Tsohon Ministan na birnin tarayya Abuja ya ce zai tuntubi masu ta-cewa a harkar kasar kafin ya bayyana matsayar da ya dauka a kan neman mulkin Najeriya.

A ba Arewa tikitin PDP

Sanata Bala Mohammed yake cewa adalcin da jam’iyyar PDP za tayi shi ne ta fito da ‘dan takararta daga yankin Arewacin Najeriya domin ya gwabza da APC.

Da yake kare matsayin da ya dauka, Mai girma gwamnan ya ce takwarorinsa da ke mulkin jihohi ba su da wani uzurin tsaida ‘dan takara daga bangaren Kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel