Kotu ta sharewa Kwankwasiyya hanyar takarar Shugaban PDP a Arewa a sa’ar karshe

Kotu ta sharewa Kwankwasiyya hanyar takarar Shugaban PDP a Arewa a sa’ar karshe

  • An samu kotu da ke Zaria, a jihar Kaduna da ya hana Bello Hayatu Gwarzo shiga takara a zaben PDP
  • Alkali ya ce ba zai yi yiwu Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya fito zabe bayan jam'iyya ta dakatar da shi ba
  • Wannan hukuncin zai taimakawa bangaren Kwankwasiyya da za su yi takara da tsohon ‘dan majalisar

Kaduna - Babban kotun da ke zama a garin Zaria, jihar Kaduna, ta dakatar da daya daga cikin masu neman mukamin shugaban jam’iyyar PDP na Arewa.

Jaridar Daily Trust ta ce kotu ta hana Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya shiga duk wata harkar jam’iyyar PDP har sai zuwa lokacin da aka karkare shari’arsa.

Sanata Gwarzo yana cikin masu neman takarar shugaban PDP na yankin Arewa maso yamma, ya yi shirin ya gwabza da Mohammed Jamo a zaben da za ayi.

Kara karanta wannan

Jerin matsaloli 6 da Kwankwaso yake bukatar ya tsallake kafin ya shiga Aso Rock a 2023

Alkali mai shari’a K. Dabo ya dakatar da PDP daga daukar Bello Hayatu Gwarzo a matsayin daya daga cikin ‘ya ‘yanta, ko a kyale shi ya shiga harkar jam’iyya.

“An sa takunkumin hana (Gwarzo) daga shiga harkar (PDP) ko neman kujera a zaben da za ayi na shugaba na Arewa maso yamma, sai an gama shari’a.”
Kotu ta sharewa Kwankwasiyya hanya a takarar Shugaban PDP a Arewa a sa’ar karshe
Kwankwaso mai goyon bayan Mohammed Jamu Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ana bada umarni ga (PDP) ya tabbatar cewa an tafi a tsarin da ake kai na dakatar da (Gwarzo) har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin karshe a kan karar sa.”
“Za a koma kotu a ranar 14 ga watan Maris, 2022 domin a saurari karar da aka shigar.” - K. Dabo

PDP ta yi magana

Jim kadan bayan samun labarin wannan hukunci sai shugaban jam’iyyar PDP na reshen jihar Kaduna, Shehu Bala Sagagi ya fitar da jawabi a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Ba kullum ake kwana a gado ba: PDP ba za ta ba Atiku takara a 2023 ba – Tsohon Gwamna

Shehu Sagagi ya zargi Sanata Gwarzo da yi wa jam’iyya makarkashiya a zaben 2019. Jam’iyyar PDP ta ce a karshe gwamna Abdullahi Ganduje ya yi masu sakayya.

Shugaban jam’iyyar ya ce an dakatar da tsohon ‘dan majalisar daga matakin karamar hukuma da na jiha. Solacebase ta ce wannan dakatarwa ce kotu ta tabbatar jiya.

Rikicin cikin gidan PDP

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya ke goyon bayan Mohammed Jamo, bai tare da tsohon Sanatan Arewacin jihar Kano.

Kwanakin baya kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso ya zargi gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal da katsalandan a harkokin PDP a jiharsu ta Kano.

Ku na sane cewa sabanin nan ya jawo aka daga zaben na mataimakin shugaban PDP na kasa na shiyyar Arewa maso gabas, inda Kwankwaso da Tambuwal suka fito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel