PDP: Ana musayar yawu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal

PDP: Ana musayar yawu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal

- Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar PDP reshen arewa maso yamma inda ake musayar yawu tsakanin Kwankwaso da Tambuwal

- Kwankwaso ya zargi gwamna Tambuwal da yin katsalandan a harkokin jam’iyyar a jihar Kano

- Sai dai kuma gwamnan na Sokoto ya nisanta kansa da zargin da Kwankwaso ya yi masa na cewa yana da hannu a siyawa Sanata Bello Hayatu Gwarzo fam

Ga dukkan alamu, sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen arewa maso yamma, yayinda Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da yin katsalandan a harkokin jam’iyyar a jihar Kano.

Kwankwaso wanda ya kasance daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar a yankin ya zargi Tambuwal da hada kai da wasu yayan jam'iyyar na Kano da ke adawa da shi da mutanensa don taimaka musu su samu shugabancin jam'iyyar na Arewa maso Yamma.

KU KARANTA KUMA: Zan bar Kaduna da zaran na kammala wa’adin mulkina - El-Rufai

PDP: Ana musayar yawu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal
PDP: Ana musayar yawu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal Hoto: BBC.com
Asali: UGC

A hirarsa da sashin Hausa na BBC Kwankwaso ya ce:

"Abin takaici shi ne akwai shi gwamna na Sokoto, wanda a ra'ayinsa yace bai kamata mu musamman mu yan Kwankwasiyya a bamu wadan nan mukamai ba."

Kan cewa ko Tambuwal ya fadi hakan ko zargi suke yi, Kwankwaso ya ce: "Kwarai da gaske abunda ya faru abunda muke da shi mu da Jigawa shine muna da shugaba na wannan sashi.

"Toh babban matsalar shine a cikinmu akwai wadanda aka samu matsaloli da su, cewar sun yi mana anti-pati.

"Toh saboda haka da wannan fam ya shigo ni na tura an siyo mana fama, amma abunda ya sa magana ta fito na shi Tambuwal, ya siye wannan fam a wurin wannan taro da muka yi, an kawo rahoto cewa shine ya bayar da kudi aka siyo masa fam kuma aka ba shi Sanata Bello Hayatu."

Game da abunda ya kawo Tambuwal harkar siyasar Kano, Kwankwaso ya ce: “Abunda ya kai shi (Tambuwal) shine gaggawa, saboda mutane da yawa suna ganin abunda yake yi ya shafi ta shekara r 2023. Yana ganin idan aka ba Kano kamar mu zai taimaka mana.”

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi sharhi akan batutuwan da suke hana matarsa bacci

To sai dai a nasa bangaren, gwamna Aminu Tambuwal ya karyata wannan zargi inda ya ce "duk wanda yake da sha'awa ya fito ya yi takara, toh ya fito ya yi takara".

Ya kuma nisanta kansa da zargin da Kwankwaso ya yi masa na cewa yana da hannu a siyawa Sanata Bello Hayatu Gwarzo fam.

Asali: Legit.ng

Online view pixel