Ba kullum ake kwana a gado ba: PDP ba za ta ba Atiku takara a 2023 ba – Tsohon Gwamna

Ba kullum ake kwana a gado ba: PDP ba za ta ba Atiku takara a 2023 ba – Tsohon Gwamna

  • Da kamar wahala Atiku Abubakar ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 2023
  • Wani babban jagora a jam’iyyar hamayyar ya ce zai yi wahala a ce PDP ta sake ba Atiku tutarta
  • A halin yanzu Gwamnonin PDP masu-ci sun sha gaban kowa a jam’iyya, kuma ba su tare da Atiku

Abuja – Wani babba a jam’iyyar hamayya ta PDP, ya ce da kamar wuya Atiku Abubakar ya rike tutar jam’iyya a zaben shugaban kasa da za ayi a 2023.

A ranar Talata, 8 ga watan Fubrairu 2022, jaridar Vanguard ta rahoto wannan jigo na jam’iyya yana cewa gwamnonin PDP su na kara karfi a jam’iyya.

A hirar da aka yi da wannan tsohon gwamna na yankin Arewa maso yamma, ya bayyana cewa gwamnoni ne su ke rike da PDP, kuma sai yadda suka yi.

Kara karanta wannan

Ya kamata PDP ta karɓe mulkin Najeriya, zaman lafiya ya gagara, inji gwamnan PDP

Zai yi wahala Atiku ko waninsa ya iya doke wadannan gwamnoni masu-ci a zaben fitar da gwani.

Ana yi masa hannunka mai sanda

Kamar yadda ya bayyana, jagoran na PDP ya ce gwamnonin jihohi biyu sun fadawa Atiku gaskiya a ‘yan kwanakin nan, su na nuna masa ya hakura da 2023.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya fito gar-da-gar ya na cewa Atiku Abubakar yana gaba da su a siyasa, kuma ya cancanta da mulki amma ya tsufa.

Zaben 2019
Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Aminu Tambuwal Hoto: PDP
Asali: Facebook

Haka zalika, rahoton ya ce an ji gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya fadawa tsohon mataimakin shugaban kasar cewa mutane sun yi fushi da shi.

Kowa da lokacinsa

“Atiku ya yi izna da wadannan hannunka mai sandan da ake yi masa, ya dauki matakin da ya dace domin abubuwa sun canza a wannan lokaci.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Na ki goyon bayan Tofa, Rimi, Buhari na zabi Abiola, Obasanjo da Jonathan

“A wasu wurare, za a yi mamakin jin irin wannan magana, amma gaskiyar kenan. Gwamnonin jihohi ne yanzu ke rike da jam’iyyar PDP gam.”
“Ba tare da goyon bayan gwamnonin nan ba, kusan ba zai yiwu mutum ya iya samun takara a karkashin jam'iyyar PDP ba.” - Jigon jam'iyya

Gwamnonin jam’iyyar sun nunawa Atiku Abubakar da Bukola Saraki iyakarsu a zaben shugabannin da aka yi kwanaki, bayan tunbuke Uche Secondus.

Zuwan Atiku Benuwai

Ku na da masaniya cewa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya hadu da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar a Makurdi.

Alhaji Abubakar ya ziyarci jihar Benuwai, har ya taimakawa ‘yan gudun hijira. Ortom ya yi amfani da wannan dama ya fadawa Atiku ya yi watsi da mutanen Benuwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel