Gwamnan Bayelsa zai hada Mataimakin Shugaban kasa, Jonathan da Gwamnonin PDP 5

Gwamnan Bayelsa zai hada Mataimakin Shugaban kasa, Jonathan da Gwamnonin PDP 5

  • Nan da ‘yan kwanaki kadan Douye Diri zai cika shekaru biyu a matsayin Gwamnan jihar Bayelsa
  • Za a shirya gagarumin biki domin murnar wannan rana ta hanyar kaddamar da wasu kwangiloli
  • An gayyaci irinsu Farfesa Yemi Osinbajo da Goodluck Jonathan wajen wannan biki da bude ayyukan

Bayelsa – Jaridar The Nation ta ce jihar Bayelsa za ta cika, ta batse yayin da aka fara shirye-shirye bikin cikar gwamna Douye Diri biyu a karagar mulki.

A ranar 14 ga watan Fubrairun 2022 ne Mai girma Douye Diri yake cika shekaru biyu a kan mulki. Amma an fara bukukuwan zuwan wannan rana tun yanzu.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan su na cikin wadanda aka gayyata zuwa wajen bikin.

Sauran wadanda gwamna Douye Diri ya gayyata sun hada da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, sai tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Masu son kujerar Buhari basu san dumin da ke tattara da ita ba, inji Sanusi

‘Yan majalisar tarayya, malaman addini da manyan kasa za su halarci jihar Bayelsa domin kaddamar da wasu daga cikin ayyukan gwamnatin Sanata Diri.

Za ayi dogon biki

A wani jawabi da kwamishinan ayyuka, tsare-tsare da dabaru na jihar Bayelsa, Ayibaina Duba ya fitar, an ji cewa za a shafe tsawon makonni biyu ana bukukuwa.

Manyan kasa
Osinbajo, Jonathan da Atiku Hoto: dailypost.ng
Source: UGC

Gwamnonin Oyo, Akwa Ibom, Bauchi, Ribas, Sokoto; Seyi Makinde, Udom Emmanuel, Bala Mohammed, Nyesom Wike, Tambuwal za su kaddamar da ayyuka.

Haka zalika tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan da irinsu Ifeanyi Okowa, Sanata Seriake Dickson da Ayu za su kaddamar da kwangilolin da aka gama.

Osinbajo zai kaddamar da aiki

Blueprint ta ce Mai girma Osinbajo zai kaddamar da aikin gadar nan da za ta hada garin Oporoma inda nan ne hedikwatar kasar Ijaw da mutanen yankin Angiama.

Garin Angiama ya na kan hanyar birnin Yenagoa zuwa Oporoma. Osinbanjo zai kai ziyara ne zuwa Bayelsa a ranar 17 ga watan nan domin kaddamar da aikin.

Kara karanta wannan

Ya kamata PDP ta karɓe mulkin Najeriya, zaman lafiya ya gagara, inji gwamnan PDP

Sauran ayyukan da za a bude sun hada da gadojin Yenagoa City, Elebele da Nenbe, Akwai kuma tituna a Igbedi da cibiyar koyon kasuwanci da wasu gidajen gwamnati

Shawarar Yemi Osinbajo

A ranar Litinin ne aka ji mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya fadawa al’umma su guji zaben ‘Dan siyasa saboda kurum addinsu ko kuma yankinsu daya.

Yemi Osinbajo ya halarci taron kwararrun 'yan jam'iyyar APC da aka shirya a Aso Villa, inda ya gargadi 'yan siyasa masu neman raba kan jama'a da cewa za su sha kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng