Yemi Osinbajo ya fadakar da jama’a a kan ‘yan siyasan da za su nesanta a zaben 2023

Yemi Osinbajo ya fadakar da jama’a a kan ‘yan siyasan da za su nesanta a zaben 2023

  • Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya halarci taron kwararrun 'yan jam'iyyar APC
  • An shirya wannan taro a Aso Villa domin ayi magana a kan rawar da kwararru za su taka a mulki
  • Yemi Osinbajo ya ba mutane shawara su guji zaben ‘yan siyasa saboda ra’ayin addini ko kabilanci

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ba mutanen Najeriya shawara su guji ‘yan siyasar da suke amfani da kabilanci wajen neman mulki.

Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro na kwararrun 'yan jam'iyyar APC da ake yi a fadar Aso Villa.

Daily Trust ta ce an yi wa taron take da “The Role of Professionals in Politics and National Building” domin yin bayanin muhimmancin kwararru a siyasa.

Kara karanta wannan

Lissafin Tinubu zai canza, Osinbajo yana daf da tsayawa takarar shugaban kasa

Mai girma Yemi Osinbajo ya ce dole ne kwararrun mutanen da suka shiga siyasa su dage domin su nunawa al’umma yadda ake tafiyar da sha’anin shugabanci.

A ajiye bambanci a gefe guda - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar ya ce babu bukatar a samu kwararru a harkar siyasa da suka buge wajen raba kan al’umma da addini, kabilanci ko wani son ra’ayi.

A cewar Osinbajo, amfanin zama kwararre shi ne ana yi wa mutum kallon cancanta da sanin aiki.

Yemi Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jaridar ta rahoto Farfesa Osinbajo ya na kira da babban murya ga dukkanin masu ruwa da tsaki, su hada-kai domin a kawo mafitar matsalolin da suka addabi kasar.

“Babu wanda zai bari likitan bogi ya duba shi saboda kurum addininsu guda, ko ya cigaba da kai gyaran mota wajen rubabben makaniki saboda ‘dan kabilarsa ne.”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Mayakan ISWAP 25 sun nitse a kogin Marte yayin da suke guje ma harin sojoji

“Misali idan aka fada mani cewa wanda zai tuka jirgi na bai kware sosai ba, amma mutumin Ikenne ne – garinmu, babu shakka ba zan hau wannan jirgin saman ba.”

- Yemi Osinbajo

Da wadannan misalai ne Osinbajo ya ba jama’a shawara su rika neman wanda ya dace idan aka tashi zaben shugaba, su daina amfani da son kai da bangaranci.

Tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura ya halarci wannan taro da aka yi. Tanko Al-Makura yana cikin masu neman shugabancin APC.

Siyasar PDP a 2023

A jiya wani jagoran jam'iyyar PDP ya tada hankalin magoya bayan Atiku Abubakar, ya ce ba su da tuta a 2023 saboda jam’iyyar adawar ta na hannun Gwamnoni.

Wannan jigo wanda ya yi gwamna a PDP ya bayyana cewa an fara yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa hannunka mai sanda a kan batun neman takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel