Duk da ya jarraba sa’a sau 3 babu nasara, Sanatan APC zai sake neman Shugaban kasa

Duk da ya jarraba sa’a sau 3 babu nasara, Sanatan APC zai sake neman Shugaban kasa

  • Alamu su na nuna cewa tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha zai sake jarraba farin jininsa
  • Sanata Rochas Okorocha ya na shirin ya nemi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC
  • A farkon makon gobe Sanatan na Imo zai yi wa Duniya jawabi, ya bayyana matsayar da ya dauka

Abuja - A wani rahoto, Leadership ta ce akwai yiwuwar Sanatan na Imo ta yamma ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023.

Wata kungiya da ke goyon bayan Rochas Okorocha ya nemi kujerar shugaban kasa, New Nigeria Movement (NNM) ta kyankyasa wannan a makon da ya wuce.

Daya daga cikin jagororin tafiyar New Nigeria Movement, Farfesa Aliyu Abdullahi Jibia ya ce Okorocha zai yi wa Duniya jawabi a ranar 31 ga watan Junairu.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

A cewar Farfesa Aliyu Jibia, Okorocha zai yi jawabi a taro a ranar Litinin mai zuwa.

“Wadanda aka gayyata wajen taron manema labaran sun hada da kungiyoyin addini, kungiyoyi masu zaman kansu, matasa, mata, ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa.”

- Aliyu Abdullahi Jibia

Taron manema labarai

Jaridar New Telegraph ta rahoto Aliyu Abdullahi Jibia yana cewa za ayi wannan taro ne a Abuja.

Tsohon Gwamnan jihar Imo
Rochas Owelle Okorocha da Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sanata Owelle Rochas Okorocha zai yi wa mutanen Najeriya da ke gida da kasar waje, magoya bayansa da sauran jama’a jawabi a wannan gagarumin taro.

Okorocha ya cancanta

Farfesa Jibia ya ce Jekan na Sokoto, kuma Maga-Alherin Hausa, da Owellen kasar Ndi Igbo watau Okorocha yana cikin wadanda aka kafa APC da su a 2013.

Baya ga haka tsohon gwamnan ‘dan kasuwa ne kuma attajiri wanda ya dage wajen ilmantar da yaran talaka, sannan ya yi digiri har da digirgir a harkar boko.

Kara karanta wannan

Zaben APC: ‘Yan Jam’iyya a Arewa sun tsaida ‘Dan amanar Buhari a matsayin ‘dan takararsu

Tarihin takarar Okorocha

Bayan zaben 1999 ne Rochas Okorocha ya koma APP, ya nemi tikitin zama shugaban kasa a jam’iyyar amma bai ci nasara ba, daga nan sai ya koma PDP.

A 2005 Rochas Okorocha ya kafa jam’iyyar AA domin ya samu damar takarar shugaban kasa. A karshe ya nemi tikitin PDP, a nan ma dai bai yi nasara ba.

A zaben fitar da gwani na APC a 2014, Okorocha na cikin wadanda su ka nemi tikitin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel