Ya yi karatu a makarantarmu – Jami’ar Amurka ta raba gardama kan Digirin Bola Tinubu

Ya yi karatu a makarantarmu – Jami’ar Amurka ta raba gardama kan Digirin Bola Tinubu

  • Jami’ar nan ta Chicago State University ta tabbatar da cewa Asiwaju Bola Tinubu tsohon dalibinta ne
  • Hakan zai kawo karshen zargin da ake yi wa tsohon gwamnan na Legas cewa bai yi karatun digiri ba
  • A wata takarda da wani jami’in makarantar ya aiko, ya ce babu shakka sun taba koyar da Bola Tinubu

United States - Jami’ar jihar Chicago wanda aka fi sani da Chicago State University a kasar Amurka, ta yi magana game da batun karatun Asiwaju Bola Tinubu.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 26 ga watan Junairu 2022, inda aka ji jami’ar ta na gasgatar ikirarin Bola Tinubu na cewa ya yi karatunsa makarantar.

Babban jami’in da ke kula da sakamakon jarrabawa, daukar sababbin dalibai da tantance takardun digiri na jami’ar, Beverly Poindexter ya tabbatar da wannan.

Kara karanta wannan

Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

Mista Poindexter ya shaidawa jaridar wannan da yake bada amsar tambayar da aka aika masa ta imel.

An tuntubi makarantar Amurkan domin ta warware rudanin da aka shiga a Najeriya, sai wannan jami’i ya bada tabbacin cewa Bola Tinubu ya yi karatunsa a Jami’ar.

Bola Tinubu
Jagaban Bola Tinubu Hoto@AsiwajuTinubu
Asali: Twitter

Abin da jami'ar ta ce

Sannan makarantar ta bada shafin yanar gizon da za a samu karin bayani a kan lamarin. Hakan zai sa a birne zargin da ake yi wa Tinubu na cewa bai je marakantar ba.

"Mista Tinubu ya halarci jami’armu, idan kuma ana neman karin bayani, sai a ziyarci shafin studentclearinghouse.org domin a aika bukatar da ake nema."

-Beverly Poindexter

An yi haka a 1999

A wata makamaciyar wannan wasika da magatakardar jami’ar a wancan lokaci, Lois Davis ya rubuto a Agustan 1999, ya yi magana a kan digirin ‘dan siyasar Najeriyan.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

“Ku sani cewa Bola A. Tinubu ya halarci jami’ar Bola A. Tinubu daga Agustan 1977 zuwa watan Yunin 1979.”
“Ya samu shaidar digirin B. Sc a ilmin kasuwanci a ranar 22 ga watan Yuni, 1979. Ya kware ne a fannin akawu.”

Siyasar 2023

A jiya kun ji cewa Muhammadu Buhari zai iya shiga tsaka mai wuya idan mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce yana sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a APC.

Tun tuni Bola Tinubu ya fito ya fadawa Duniya cewa zai nemi shugabancin Najeriya a 2023. Ana ganin Tinubu ya taimakawa Buhari wajen samun tikitin APC a zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel