Gwamnan Kudu ya zugo Gwamnoni domin a yaki Atiku, Saraki da manyan Arewa a PDP a 2023

Gwamnan Kudu ya zugo Gwamnoni domin a yaki Atiku, Saraki da manyan Arewa a PDP a 2023

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya dage wajen ganin ‘Dan kudu PDP ta tsaida a zaben shugaban kasa
  • Ana tunanin Gwamna Nyesom Wike zai fafata da jiga-jigan PDP na yankin Arewa wajen samun tikiti
  • A ‘yan makonnin nan, Wike ya yi zama da gwamnonin PDP domin ganin yadda jam’iyya za ta zama a hannunsu

Rahotanni daga Daily Trust sun nuna cewa Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya fito gadan-gadan domin ya yaki kusoshin PDP daga Arewacin Najeriya.

Nyesom Wike yana neman yadda zai jikawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Bukola Saraki, da irinsu Rabiu Kwankwaso aiki a zaben 2023.

Majiya ta shaidawa jaridar cewa gwamnan na jihar Ribas wanda kusan shi kadai ne yake daukar dawainiyar jam’iyyar hammayar, ya fara tuntubar abokan aikinsa.

Wike yana kokarin ganin jam’iyyar PDP ta fito da ‘dan takarar shugaban kasa daga kudu a 2023. Jaridar The Nation ta ce gwamnoni na kara rike iko da jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Tseren shugabancin APC ya koma tsakanin Sanatoci 2, da tsohon Ministan Buhari

WIke ya na zama da Gwamnoni

A makon da ya gabata ne Gwamna Wike ya zauna da kusan duka gwamnonin PDP a gidan gwamnati da ke Fatakwal, an yi zaman ne domin fara shirin 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wike ya hadu da gwamnonin adawan a fadarsa ne bayan ziyarar da ya kai wa takwarorinsa na jihohin Bauchi, Adamawa, Sokoto, Abia, Enugu, Oyo da kuma Bayelsa.

Gwamnoni
Gwamnonin PDP bayan wani taro Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Rahoton ya ce Wike ya na neman jawo gwamnoni biyar da za su dafa masa. Ana tunanin ya na tare da gwamnonin Benuwai, Enugu, Oyo, Abia da na jihar Adamawa.

A halin yanzu babu wanda zai iya takawa Nyesom Wike burki a jam’iyyar PDP domin shi yake rike da majalisar NWC tun bayan da ya dage aka kori Uche Secondus.

Gwamnonin PDP

Gwamnonin PDP masu-ci su ne: Okezie Ikpeazu (Abia), Ahmadu Fintiri (Adamawa), Udom Emmanuel (Akwa Ibom), Bala Muhammed (Bauchi), da shi Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun zugo ‘Yan Majalisa su bankara Buhari a kan gyara dokar zabe

Sai Douye Diri (Bayelsa), Samuel Ortom (Benue), Sanata Ifeanyi Okowa (Delta), Godwin Obaseki (Edo), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), da kuma Injiniya Seyi Makinde (Oyo).

Ragowar gwamnonin adawan su ne: Aminu Tambuwal (Sokoto) and Darius Ishaku (Taraba).

Masu neman tikitin 2023

A halin akwai gwamnonin Arewa masu ci biyu da suke hangen takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP - Aminu Waziri Tambuwal da gwamna Bala Mohammed.

Baya ga Atiku Abubakar, ana ganin cewa irinsu tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Rabiu Musa Kwankwaso su na sha’awar tsayawa takara a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel