Jerin Gwamnonin 7 da ke harin shugabancin kasa a zaben 2023

Jerin Gwamnonin 7 da ke harin shugabancin kasa a zaben 2023

  • Ba sabon abu ba ne don gwamna ya zarce zuwa fadar shugaban kasa domin an ga irinsu Ummaru ‘Yar’adua, ko ma a ce shugaba Muhammadu Buhari
  • Yayin da aka fara buga gangar siyasa a Najeriya, akwai wasu gwamnonin da ake ganin za su iya neman takarar shugaban kasar nan a babban zaben da za ayi
  • A wadannan gwamnoni akwai wadanda sun kammala wa’adinsu zuwa 2023, akwai wadanda kuma za su yi karambani ne tun da ba za su yi saki-na-dafe ba

Ga jerin wadannan gwamnoni nan da Legit.ng Hausa ta kawo maku a wannan rahoto:

1. Aminu Tambuwal

Masu hasashe su na ganin Aminu Waziri Tambuwal zai nemi tikitin shugaban kasa a PDP kamar yadda ya nema a 2019. Tun 2015 Tambuwal yake da wannan buri.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan siyasan Kudu na neman canza lissafin APC, Tinubu na hada-kai da abokan fada

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya nemi tutar PDP a zaben da ya wuce, har ya zo na biyu.

2. Dave Umahi

Gwamnan jihar Enugu, David Umahi ya bar PDP zuwa APC ne saboda ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 2023. Gwamnan na Enugu ya kuma fito da burinsa a fili.

3. Kayode John Fayemi

Dr. Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya na daga cikin wadanda ake ganin zai iya tsayawa neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC domin ya gaji Buhari.

Gwamnonin Jam’iyyun PDP
Gwamnonin PDP Wike da Tambuwal Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

4. Bala Mohammed

Duk da cewa yanzu yake wa’adinsa na farko, an fara yada cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed zai tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

5. Nyesom Wike

Wani gwamnan adawa a wannan rukuni shi ne Nyesom Wike na Ribas. Kamar Bala Mohammed, shi ma Wike ya rike Ministan tarayya a gwamnatin Jonathan.

Kara karanta wannan

An gano dalilin kus-kus din Gwamnan APC da Tinubu sa'a 48 da ayyana niyyar takara

6. Seyi Makinde

Seyi Makinde bai dade da zama gwamna ba sai aka fara yi masa hangen kujerar shugaban kasa. Gwamnan na Oyo shi kadai ne gwamnan PDP a kudu maso yamma.

7. Yahaya Bello

Na karshe a gwamnonin cikin wannan jeri shi ne gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi wanda duk alamu sun nuna zai nemi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Har ila yau akwai gwamnoni irinsu Ben Ayade da ake ganin su na harin 2023. Wasu kuma su na cewa Babangida Zulum zai yi kyau da mataimakin shugaban kasa.

Tinubu zai dace?

Dazu muka kawo maku jerin wasu manyan cikas da Bola Tinubu zai fuskanta a yunkurinsa na karbar mulki daga hannun shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Bola Ahmed Tinubu yana cikin manyan ‘yan siyasan da ake ji da su, amma akwai alamun tambaya game da yadda ya yi kudinsa, da ingancin takardun karatunsa.

Kara karanta wannan

Addini, rashin lafiya, da matsaloli 5 da Tinubu zai fuskanta a neman Shugaban Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel