Magana ta canza: Sanatan APC ya ce yanzu da shi za a nemi takarar Shugaban kasa a 2023

Magana ta canza: Sanatan APC ya ce yanzu da shi za a nemi takarar Shugaban kasa a 2023

Shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya, Orji Uzor Kalu zai nemi shugabanci a 2023

Sanata Uzor Kalu ya ce ya canza shawara a game da shirin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa

Kafin yanzu Sanatan na Abia ya fadawa Bola Tinubu, Anyim da su Gwamna Umahi ba zai yi takara ba

Abuja - Punch ta rahoto Orji Uzor Kalu yana cewa a baya ya fadawa irinsu Sanata Anyim Pius Anyim da David Umahi cewa ba zai nemi shugabancin kasa ba.

Amma da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Silverbird Television a ranar Juma’a, 21 ga watan Junairu 2022, Sanatan ya ce ya canza shawara a halin yanzu.

A cewar Orji Uzor Kalu, mutane daga duka bangarorin kasar nan sun same shi, sun kuma roke shi ya fito neman titikin takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Dan marigayi Abacha na shirin shiga APC ne? Babban Sanatan APC ya magantu, ya wallafa hotunansu tare

Tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana cewa kwarewarsa da sanin aikinsa mutane suka duba, don haka su ka nemi ya shiga cikin wadanda za su nemi mulki.

Sanata Orji Kalu yake cewa ya yi imani zai iya shawo kan rashin tsaro da matsalar tattalin arziki.

Sanatan APC da Tinubu
Bola Tinubu da Orji Uzor Kalu Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Abin da na fada a baya - Sanata Kalu

“Ban so in shiga takarar nan a da ba. A lokacin da na hadu da Sanata Tinubu, na fada masa ba zan yi takara. Da na hadu da Gwamna Umahi, na fada ba zan yi takara ba.”
“A lokacin da hadu da Sanata Anyim Pius Anyim, shi ma na fada masa ba zan yi takara ba.” - Kalu

Sai me ya faru?

“’Yan kwanakin kadan bayan na zauna da su, dattawan yamma da na Arewa, da na kudu maso gabas da na Neja-Delta sun same ni a ranar 5 ga watan Junairu.”

Kara karanta wannan

Sanatocin jihar Katsina 2 sun yi watanni 25 a Abuja, ba su kawo korafi ko shawara 1 ba

“Na bar kauyenmu na je wasu wurare, na hadu da manyan Arewa da Yamma a Legas da Warri, sai na dawo kauyenmu na Igebere, na hadu da dattawan kasarmu.”

Daga nan sai shawara ta canza, Uzor Kalu ya ce ya fara ganin yiwuwar fitowa takara, zai yi zama da su nan gaba, daga nan sai ya shaidawa Duniya zai nemi mulki.

A game da karon da za ayi, Kalu ya ce su na da kyakkyawar alaka, kuma Tinubu ba zai zama barazana gare shi ba, a cewarsa ya taimakawa tazarcen Tinubu a 2003.

“Na taimakawa neman tazarcesa a 2003, wannan ya jawo matsalata da Obasanjo. Duk mun zama daya, ba za mu yi fada saboda da siyasa ba, kowa yana da hajarsa.

Femi Gbajabiamila ya na yi wa wani aiki

Bala Ibn Na’Allah ya fito ya na cewa shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ne ya shigo da sharadin ‘yar tinke a dokar zabe ta bayan fage.

Kara karanta wannan

Ba zan taba sukar Tinubu ba, aboki na ne: Orji Uzor Kalu

Sanatan na jihar Kebbi ya ce shugaban majalisar wakilan ya dauki wannan matsaya ne saboda a taimakawa wani ‘dan siyasa, kuma a takawa gwamnoni burki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel