Ta yi tsami an ji: Sanatan APC ya tona wanda ya cusa tsarin ‘yar tinke a kudirin gyara zabe

Ta yi tsami an ji: Sanatan APC ya tona wanda ya cusa tsarin ‘yar tinke a kudirin gyara zabe

  • Bala Ibn Na’Allah ya bayyana yadda batun ‘yar tinke ya shigo cikin kudirin gyara dokar zaben Najeriya
  • Wannan ba aikin kowa ba ne illa shugaban majalisar wakilai na kasa, Femi Gbajabiamila inji Sanatan
  • Sanata Ibn Na’Allah ya na ganin an kawo sharadin daga baya ne saboda ana neman taimakawa wani

Abuja - Sanata Bala Ibn Na’Allah ya zargi shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da kawo shawarar ‘yar tinke a kudirin gyara dokar zaben kasar nan.

Daily Trust ta rahoto Bala Ibn Na’Allah ya na cewa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya kawo wannan sharadi a kudirin zaben saboda a taimakawa wani mutum.

Sanatan na yankin Kebbi ta Kudu ya shaidawa gidan talabijin na Channels TV wannan a lokacin da aka gayyace shi zuwa shirin Sunrise Daily a jiya da safe.

Kara karanta wannan

Tseren shugabancin APC ya koma tsakanin Sanatoci 2, da tsohon Ministan Buhari

Da yake bayani a ranar Alhamis, shugaban kwamitin kula da aikin sojojin sama na majalisar dattawan bai bayyana wanda aka nemi ayi wa alfarmar ba.

Ba ayi tunani da kyau ba - Na ' Allah

“Mu na jin labari cewa an kawo dokar (‘yar tinke) ne saboda wani mutum guda. Gaskiya ban sani ba, amma dole in ce ba ayi tunani sosai ba."
Femi Gbajabiamila
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila Hoto: @femigbaja
Asali: Twitter

“Maganar zaben ‘yar tinke ta shigo majalisar wakilan tarayya ne a karshe a lokacin da ake shirin karbar rahoton kwamitocin harkar zabe.”
“Abin da hakan ke nufi shi ne ba a tattauna kan wannan maganar a kwamitin majalisa, daga baya aka shigo da ita a matsayin kwaskwarima"

- Bala Ibn Na’Allah

Sanatan ya zargi Gbajabiamila da wannan danyen aiki, ya ce an yi hakan ne domin a tsare ‘yan majalisa daga gwamnonin da suke baba-kere, su rike komai.

Kara karanta wannan

EFCC ta na binciken mutum 5 a cikin masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC

Na Allah ya ce shugaban majalisar wakilai ya yi bakin kokarinsa domin kare matsayar da ya dauka.

A karon farko maganar ba za ta je ko ina ba saboda son rai ya shigo cikin aikin ‘yan majalisar, wanda hakan ya sabawa rantsuwar da suka yi inji Na’Allah.

Tinubu ya samu goyon baya

A makon nan ne aka ji cewa wasu tsofaffin shugabannin kananan hukumomi na jihar Legas sun fara yi wa Bola Tinubu yakin zaben shugaban kasa a zaben 2023.

‘Yan Grassroots Network for Asiwaju Bola Tinubu sun ce ba za su yi butulci, su manta da alherin da tsohon gwamnan na Legas ya yi masu tsakanin 1999 da 2003 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel