A karo na biyu, Bola Tinubu ya kara yi wa Talakawan Najeriya babban alƙawari da zaran ya ɗare mulki a 2023

A karo na biyu, Bola Tinubu ya kara yi wa Talakawan Najeriya babban alƙawari da zaran ya ɗare mulki a 2023

  • An tabbatar wa yan Najeriya cewa duk wasu matsalolinsu na kuɗin makaranta da kuɗin neman lafiya zasu koma hannun gwamnati daga 2023
  • Bola Tinubu, jagoran APC mai mulki na ƙasa, yace zai tabbatar yan Najeriya sun samu ilimi kyauta da zaran ya hau mulki a 2023
  • A cewar Tinubu, kowane ɗan Najeriya zai samu damar samun ilimi kyauta tun daga matakin Firamare zuwa jami'a

Lagos - Jagoran jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan, Bola Ahmed Tinubu, ya ɗau alakwarin cewa gwamnatinsa zata tabbatar kowane ɗan Najeriya ya samu ilimi kyauta tun daga Firamare zuwa makarantun gaba da Sakandire.

This Day ta rahoto cewa, Tinubu, ya ƙara da alƙawarin cewa da zaran ya hau kujerar shugaban ƙasa a 2023, kowane ɗan Najeriya zai samu kulawar lafiya kyauta.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya bayyana babban abinda zai fara yi wa Talakawan Najeriya bayan zama shugaban ƙasa a 2023

Bola Tinubu
A karo na biyu, Bola Tinubu ya kara yi wa Talakawan Najeriya babban alƙawari da zaran ya ɗare mulki a 2023 Hoto: @AsiwajuTinubu
Asali: Twitter

Tinubu ya bayyana waɗan nan alkawurran ne ta bakin shugaban ƙungiyar magoya baya, Grassroots Network for Asiwaju Tinubu, Mista Ayodele Adewale.

Adewale, ya ƙara da cewa yan Najeriya ba su da ɗan takarar da ya fi Tinubu cancanta, duba da irin kwarewarsa, da kuma rayuwarsa a harkar siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace jagoran APC na da kwarewa ta ilimi, da kuma abubuwan da ya kafa tun daga ƙasar Amurka, kafin ya dawo Najeriya ya cigaba da ayyukan alkairi.

Tinubu ya baiwa yan Najeriya hakuri

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Bola Tinubu, ya baiwa yan Najeriya hakuri kan ikirarin da ya yi cewa katin zaben dake hannun su ya gama aiki.

Da yake jawabi ga wasu jiga-jigan matan jam'iyyar APC a Abuja, tsohon gwamnan Legas, ya roki matan su garzaya domin sake rijitar zaɓe kafin 2023.

Kara karanta wannan

Ba zan taba sukar Tinubu ba, aboki na ne: Orji Uzor Kalu

Yace:

"Saboda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ba zata sanar da ku a lokacin da ya dace ba, katin zabe PVC dake hannun ku, tabbas ya tashi a aiki."

A wani labarin na daban kuma Gwamna Yahaya Bello ya faɗi lokacin da zai bayyana kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, yace babu tantama zai amsa kiran da yan Najeriya maza da mata, dake sassan duniya ke masa.

Bello, ya sanar wa masoyansa dake faɗin kasa cewa a halin yanzun ya maida hankali kan babban taron APC, amma da an kammala zai amsa kiran su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel