Katin PVC: Bola Tinubu ya bada hakuri, ya nemi al’umma su yafe ‘subutar bakin’ da ya yi

Katin PVC: Bola Tinubu ya bada hakuri, ya nemi al’umma su yafe ‘subutar bakin’ da ya yi

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bada hakuri a kan kalaman da aka ji ya yi a kan batun katin PVC
  • An fitar da jawabi a madadin jigon na APC, an nemi afuwar ‘Yan Najeriya a kan wannan kuskure
  • Tinubu ya yi tuntuben harshe ne wajen cewa akwai bukatar mutane su sabunta bayanan da ke kan PVC

Abuja - Jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya bada hakuri a game da kuskuren da ya yi na cewa katin zaben PVC sun tashi aiki.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 20 ga watan Junairu, 2022 cewa Asiwaju Bola Tinubu, ya bada hakuri a kan wannan magana da ya yi.

Mai yada labari a madadin babban ‘dan siyasar ya ce Bola Tinubu ya yi kuskure a jawabin na sa. Jaridar The Nation ta fitar da wannan rahoto yau da safe.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Tinubu ya ce kowa ya sani, katin zaben da ake dashi yanzu ya riga ya lalace

A cewar hadimin, tsohon gwamnan ya yi tuntuben harshe ne da ya ce katin sun ‘tashi aiki’, ya na kokarin cewa akwai bukatar sake sabunta bayanan katin.

Jawabin da aka fitar

“A daren Talata, Asiwaju Bola Tinubu ya hadu da matan jam’iyyar APC daga Legas da sauran yankunan kasar nan da suke halartar babban taron matan APC.”
“Yayin da yake zaburar da mata a kan su duba halin da katin zaben su suke ciki, tare da ganin cewa jama’a sun yi zabe, sai ya yi amfani da kalmar ‘tashi aiki’
"Maimakon ya ce ya kamata a sabunta bayanan katin.” - Hadimin Tinubu, Tunde Rahman.
Bola Tinubu
Bola Tinubu da Shugaban INEC
Asali: Facebook

Tunde Rahman ya cigaba da cewa:

“Bayan an tuna masa, Asiwaju (Bola Tinubu) ya yi maza ya bada hakuri a kan jawabin da ya yi bisa kuskure, ya kuma ji takaicin rudanin da hakan ya iya jawowa."

Kara karanta wannan

Babu wanda ya fi Tinubu dacewa a 2023 – Tsohon Gwamnan Arewa ya kawo karfafan dalilai

"Asiwaju Tinubu ya na kuma jaddada cewa ya yabi kokari da kishin da INEC ta ke yi wajen tabbatar da an shiryawa jam’iyyun siyasa zabe na gari a Najeriya.”
“A wajen taron, Asiwaju ya karfafa bukatar mutane su shiga harkar zabe domin a bunkasa siyasar Najeriya. Sannan ya yi kira gare su su fita zabe, a rika yi da su.”

A fita filin zabe - Tinubu

A karshe Tinubu ya yi kira da babbar muarya ga mata da sauran mutane su rika fita su na kada kuri’a.

Hukumar INEC tayi martani

Ko da hukumar INEC tayi maza ta musanya ikirarin na sa, sai dai hakan ya jawo surutu tsakanin mutane musamman masu bibiyar shafukan sada zumunta na zamani.

A jiya aka ji Hukumar zabe mai zaman kanta watau INEC, ta yi wa Bola Tinubu martani kan cewa katin zabe sun daina aiki, hukumar ta ce hakan sam ba gakiya ba ne.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel