Wata sabuwa: Tinubu ya ce kowa ya sani, katin zaben da ake dashi yanzu ya riga ya lalace

Wata sabuwa: Tinubu ya ce kowa ya sani, katin zaben da ake dashi yanzu ya riga ya lalace

  • Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa katin zabe da ake dashi a yanzu ya riga ya lalace
  • Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 18 ga watan Janairu, yayin da ya karbi bakuncin shugabannin matan APC a Abuja
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya kuma bukaci jama'a su je su yi sabon katin zabe

Abuja - Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tunubu ya bayyana cewa katin zabe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta rabawa mutane sun tashi aiki.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Shugabannin matan APC a ranar Talata, 18 ga watan Janairu, a Abuja.

Da yake jawabi a taron, Tinubu ya bukaci masu zabe da su tabbata sun mallaki sabon katin zaben.

Wata sabuwa: Tinubu ya ce kowa ya sani, katin zaben da ake dashi yanzu ya riga lalace
Wata sabuwa: Tinubu ya ce kowa ya sani, katin zaben da ake dashi yanzu ya riga lalace Hoto: @Progressive4BAT
Asali: Twitter

A cikin wani bidiyo da TheCable ta wallafa a Twitter, an jiyo Tinubu yana cewa:

“Koda basu sanar da ku kan lokaci ba, katin zabenku sun tashi aiki.”

Tinubu ya kara da cewa yawan masu zabe a zabukan baya suna ta raguwa saboda lalacewar katin zaben.

A farkon watan nan ne babban jigon na APC ya ayyana aniyarsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Katin zabe ba su lalace ba, INEC ta yi Tinubu martani

Sai dai kuma, Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta ce katin masu zabe, PVC, ba su lalace ba, Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke martani, Mashawarcin Shugaban INEC, Farfesa Bolade Eyinla, ya ce wadanda suka yi rajista a baya babu bukatar su sake yi domin katin bai gama aiki ba.

Eyinla ya gargadi wadanda suka yi rajista cewa kada su sake yi domin katin da aka basu na PVC a baya-bayan nan lafiyarsu kalau kuma za su iya zabe da su, rahton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel