Salihu Lukman: Martanin Tinubu ga masu caccaka ta bayan na yi murabus daga mukami na

Salihu Lukman: Martanin Tinubu ga masu caccaka ta bayan na yi murabus daga mukami na

  • Tsohon darakta janar na kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, ya ce Tinubu ya gayyace sa bayan yin murabus din sa inda suka tattauna
  • Lukman ya ce Tinubu ya jinjina masa kan yadda ya jajirce tare da jan ragamar kungiyar kuma ya bukace sa da cigaba da ayyukan raya jam'iyyar
  • Lukman ya ce ya nisanta kan sa daga yin tsokaci kan murabus din sa tun ranar Litinin saboda ya mika takardar kuma ba a riga an amince ba

Salihu Lukman, tsohon darakta janar na kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, ya bayyana cewa ya gana da Asiwaju Bola Tinubu, jigon jam'iyya mai mulki, bayan ya yi murabus daga mukamin sa.

Lukman ya yi murabus a ranar Litinin yayin da jam'iyyar mai mulki ke tsaka mai wuya wurin tantance ranar da za ta zabi sabbin shugabannin ta, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin da yasa Gwamnatin Tarayya ba za ta dena karɓo rancen kuɗi ba, Lawan

Salihu Lukman: Martanin Tinubu ga masu caccaka ta bayan na yi murabus daga mukami na
Salihu Lukman: Martanin Tinubu ga masu caccaka ta bayan na yi murabus daga mukami na. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, Lukman ya ce ya guje wa yin tsokaci kan murabus din sa saboda jam'iyyar ba ta riga ta amince da hakan ba.

“Zan iya tabbatar mu ku da cewa da gaske ne na yi murabus kuma na mika takarda ga Abubakar Bagudu. Na nisanta kai na daga yin tsokaci ko fitar da wata takarda a kan lamarin ne saboda ina jiran amincewar su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na yi magana da shugabannin jam'iyya, 'yan uwa da abokan arziki kuma na yi musu bayanin cewa gaskiya ne na yanke hukuncin murabus daga wannan mukamin."
"Abun sha'awa, bayan jin labarin murabus di na, da yawa daga cikin shugabanni da mambobi sun kira ni domin nuna damuwar su. Daya daga cikin shugabannin jam'iyyar wanda ya kira ni shi ne Tinubu. Ya gayyace ni a ranar 17 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023

"Ya jinjina min kan yadda na dinga gangamin ganin gyaran jam'iyyar kuma ya nuna mamakin sa kan yadda wasu mambobin jam'iyyar ke caccaka ta.

Lukman ya ce shugaban kasa Muhammadu ne ya assasa kafa kwamitin zaben shugabanni inda ya kara da cewa hankula sun fara tashi yayin da kwamitin suka gagara yin zaben sabbin shugabanni.

Babbar magana: Rikicin APC ya kara kamari, daraktan kungiyar gwamnoni ya yi murabus

A wani labari na daban, Darakta Janar na kungiyar gwamnonin APC, Mohammed Salihu Lukman, ya mika takardar murabus dinsa ga kungiyar ta PGF.

Murabus din nasa a ranar Litinin ya zo ne sa’o’i 24 bayan ganawar gwamnonin jam’iyyar APC a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi a daren Lahadi.

Kokarin jin martanin daraktan na PGF bai samu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel