2023: Ganduje, da jerin ‘Yan siyasa 10 a yankin Arewa da za su karfafi takarar Bola Tinubu

2023: Ganduje, da jerin ‘Yan siyasa 10 a yankin Arewa da za su karfafi takarar Bola Tinubu

  • Bola Ahmed Tinubu yana cikin ‘yan siyasan da suka tabbatar da cewa za su nemi shiga takarar shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa na 2023
  • Bisa dukkan alamu, tsohon gwamnan na jihar Legas zai nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki a karshen shekarar nan
  • Legit.ng Hausa ta kawo jerin ‘yan siyasan Arewa da ake tunanin za su mara masa baya wajen samun nasara a zaben fitar da gwani da babban zabe na kasa

1. Kashim Shettima

Tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima ya fito ya bayyana cewa yana tare da Bola Tinubu, har kuma ya yi kira ga shugaban kasa ya mara masa baya.

2. Abu Ibrahim

Abu Ibrahim wanda ya wakilci Katsina ta kudu a majalisar dattawa yana cikin manyan abokan tafiyar Bola Tinubu tun 1992, ana tunanin yana tare da shi har gobe.

Kara karanta wannan

Wasu ‘yan takara za su fuskanci matsala a 2023, ana neman gyara dokar shiga takara

3. Babachir David Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal bai taba boye biyayyarsa ga Bola Tinubu. Jigon na APC yana cikin manyan ‘yan tafiyar Tinubu a Arewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

4. James Faleke

Hon. James Faleke mai wakiltar Ikeja a majalisar wakilai ya na cikin magoya-bayan Tinubu. Ko da yana wakiltar Legas a majalisa ne, asalin Faleke mutumin Kogi ne.

5. Lai Mohammed

Wani ‘dan siyasan da ake ganin yana tare da Bola Tinubu har gobe shi ne Alhaji Lai Mohammed. Duk da ya yi a gwamnatin Tinubu, asalinsa mutumin jihar Kwara ne.

‘Yan siyasa 11
Masu goyon bayan Tinubu
Asali: UGC

6. Abdulmumin Jibrin

Tsohon ‘dan majalisar Kiru/Bebeji a majalisar tarayya, Hon. Abdulmumin Jibrin shi ne shugaban ‘yan Tinubu Support Management Council ta magoya-bayan Tinubu.

7. Sani Saleh

Janar Muhammad Sani Saleh mai ritaya yana cikin ‘yan siyasan Arewa da suke tare da Tinubu. Tsohon sojan ya taba zama Sanatan Kaduna a karkashin jam’iyyar CPC.

Kara karanta wannan

Babu wanda ya fi Tinubu dacewa a 2023 – Tsohon Gwamnan Arewa ya kawo karfafan dalilai

8. Babangana Zulum

Wani wanda ake tunanin zai iya marawa Tinubu baya daga Arewa shi ne gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, musamman ganin ra'ayin mai gidansa.

9. Yakubu Dogara

Irinsu shugaban tafiyar CAGG, Segun Bamgbose sun ce Bola Tinubu ya dawo da Yakubu Dogara cikin APC. Ana zargin Tinubu zai dauke shi a matsayin abokin tafiyarsa.

10. Boss Mustafa

An dade ana rade-radin cewa Boss Mustafa zai yi takara tare da Tinubu a 2023. Jiga-jigan APC kamar Umar Duhu su na ganin hakan ta na iya faruwa a zabe mai zuwa.

11. Abdullahi Umar Ganduje

Na karshe a jerin na mu shi ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wanda akwai jita-jitar zai tsaya a takarar mataimakin shugaban kasa a tikitin Tinubu a APC.

A gyara dokar zabe

Shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya na ganin lokaci ya yi da za a sake kallon sharudan da aka sa wajen shiga takarar zabe a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan siyasan Kudu na neman canza lissafin APC, Tinubu na hada-kai da abokan fada

Mafi karancin shaidar karatun da ake bukata wajen zama shugaban kasa shi ne takardar sakandare. Gbajabiamila ya ce za a iya wa tsarin mulki kwaskwarima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel