Wasu ‘yan takara za su fuskanci matsala a 2023, ana neman gyara dokar shiga takara

Wasu ‘yan takara za su fuskanci matsala a 2023, ana neman gyara dokar shiga takara

  • Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya na ganin lokaci ya yi da za a sake kallon sharudan shiga zabe a Najeriya
  • Mafi karancin shaidar karatun da ake bukata wajen zama shugaban kasa shi ne takardar sakandare
  • Shugaban majalisa ya nuna ya kamata ayi garambawul ta yadda masu ilmi za su rika jagoranci

Lagos - Yayin da ake shirin zaben 2023, shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila ya ce akwai bukatar a gyara dokar tsayawa takara a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 18 ga watan Junairu, 2022 cewa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila yana so a canza sharadin neman shugaban kasa.

Rt. Hon. Gbajabiamila ya yi jawabi na musamman a laccar yaye dalibai da aka yi a jami’ar UNILAG, inda ya bijiro da maganar samun shugabanni masu ilmi.

Kara karanta wannan

Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba

Shugaban majalisar wakilan yana gani akwai bukatar a canza doka ta yadda ba zai yiwu a ce takardar sakandare kadai ake bukata wajen neman mukami ba.

A cewar Rt. Hon. Gbajabiamila, an kawo sashe na 131(d) na tsarin mulki ne a wani lokaci dabam a tarihin kasar nan, yana ganin wannan lokaci ya wuce a yanzu.

Gbajabiamila ya kawo cikakken jawabin da ya yi a jami'ar, a shafinsa na Facebook a jiya da rana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban majalisa
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila a UNILAG Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: Facebook

An yi tuya, an manta da albasa

‘Dan majalisar yana ganin cewa canza wannan doka zai taimaka wajen gyara harkar zabe, hakan kuma zai bada damar samar da ingantaccen shugabanci a kasar.

“Kamar yadda muka rage shekarun shiga takara ga masu neman kujerun siyasa, ya kamata mu kara matakin ilmin da ake bukata.”
“Ba zai yiwu mu yi ta maganar inganta ilmi a lokacin da ake bukatar mafi karancin matakin ilmi wajen neman kujerar siyasa ba.”

Kara karanta wannan

2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Tsohon mataimakin gwamnan CBN

“Lokaci ya yi da za mu duba sashen dokar kasar nan. Mu ceci gobenmu, mu samar da al’ummar da za su zama masu fahimta.”

- Rt. Hon. Femi Gbajabiamila

A ‘yan shekarun bayan nan an kawo gyare-gyare a dokar zabe inda kokarin ‘Not too young to Run’ ya taimaka wajen ba matasa damar neman manyan kujerun siyasa.

2023 sai Bola Tinubu

A jiya aka ji Kashim Shettima yana goyon bayan Bola Tinubu ya karbi mulki, ya ce ya fi kowa cancanta da ya mulki Najeriya a cikin 'yan siyasar Kudancin Najeriya.

Daga cikin dalilan Shettima shi ne Tinubu ya rika marawa ‘Yan Arewa baya a zabukan shugaban kasa da aka yi, kuma ya ba Buhari gudumuwa wajen hawa mulki a 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel