Femi Adesina: Abin da ya sa aka ga Buhari ya je har gida ya ziyarci Tinubu kafin ya baro Ingila

Femi Adesina: Abin da ya sa aka ga Buhari ya je har gida ya ziyarci Tinubu kafin ya baro Ingila

  • Femi Adesina ya yi karin bayani kan ziyarar da Muhammadu Buhari ya kai wa Bola Tinubu
  • Fadar Shugaban kasa tace ziyarar ban-girma ne kawai Buhari ya kai wa Jigon na APC a gida
  • Hadimin Shugaban Najeriyan yace Buhari ba zai yi garajen goyon bayan wani ‘dan siyasa ba

Abuja – Babban hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ya yi karin haske game da ziyarar da Muhammadu Buhari ya ka kai wa Asiwaju Bola Tinubu.

Jaridar Punch ta ce mai taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari wajen harkar yada labarai da hulda jama’a ya ce ziyarar ba ta da alaka da siyasar 2023.

Femi Adesina yake cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya kai wa Bola Tinubu ziyara a Landan ne domin ya gaida shi saboda ana rade-radin bai da lafiya.

Kara karanta wannan

Wannan Shiryayyen Kisa Ne, Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai da Kisan Musulmai a Jos

Hadimin shugaban Najeriyar ya yi karin hasken ne da ya bayyana a wani shiri na siyasa, Politics Today da gidan talabijin nan na Channels ta saba shirya wa.

“Kwarai kuwa, ta tabbata ya kai masa ziyara, amma ziyarar barka ce kurum da fatan alheri.”
“Mun san Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana Landan kusan tun lokacin da shugaban kasa yake can, ba mu yarda da abin da muka karanta a kafofin zamani ba."

Buhari ya je har gida ya ziyarci Tinubu kafin ya baro Ingila
Bola da Shugaba Buhari a Landan Hoto: web.facebook.com/bashahmad
Asali: Facebook

“Amma mun ta jin labari game da rashin lafiyar Asiwaju Tinubu, saboda haka shugaban kasa ya kai masa ziyara ne saboda kauna.

Babu alakar ziyarar da 2023

Game da burbushin siyasa a wannan ziyara, Adesina yace lokaci bai yi ba da za a soma yakin neman zaben shugaban kasa, akwai sauran lokaci tukuna.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu zai zama shugaban kasa nagari, in ji tsohon hadimin Jonathan, ya fadi dalili

“Shugaban kasa ya na da ragowar shekaru biyu babu watanni uku a wa’adinsa. Saboda ba zai tada fara kamfe ba, shugaba Buhari ba zai taba yin wannan ba.”
“Kafin zaben 2019, mutane suka fara yi masa (Buhari) kamfe kafin hukumar INEC ta buga gangar siyasa. Shi ya fito ya ce ‘a daina garajen yakin neman zabe.”
“Saboda haka shugaban kasa da kan shi ba zai fito yana goyon bayan wani ‘dan takara yanzu ba.”

Bola Tinubu ya karbi bakuncin Shugaba Buhari

Kwanakin baya aka ji Shugaban Najeriya da Bola Tinubu sun hadu a Landan. Buhari ne na biyu da aka gani tare da Tinubu yayin da ake rade-radin bai da lafiya.

Muhammadu Buhari ne ya taka da kansa, ya kai wa Tinubu ziyara har gida kafin ya dawo Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel